Joe Biden ya nada Enoh Ebong ta rike Hukumar USTDA na rikon kwarya

Joe Biden ya nada Enoh Ebong ta rike Hukumar USTDA na rikon kwarya

- Enoh Ebong ta zama shugabar hukumar kasuwancin Amurka ta USTDA

- ‘Yar Najeriyar, Enoh Ebong za ta rike wannan kujera ne na rikon kwarya

- Ebong ta taba aiki har ta zama mataimakiyar Darekta kafin ta bar USTDA

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya nada Enoh Ebong a matsayin mukaddashiyar shugabar hukumar kasuwanci ta kasa watau USTDA.

Kamar yadda sanarwar ta bayyama, Enoh Ebong za ta koma hukumar da ta baro domin kuwa ta yi aiki a USTDA tsakanin shekarar 2004 da 2019.

A wancan lokaci wannan lauya wanda aka haifa a Najeriya ta rike mukamai da dama a hukumar.

Daga ciki ta rike lauya da kuma mataimakiyar darekta, sannan ta taba zama shugabar gudanarwa ta USTDA, kamar yadda shafin hukumar ya tabbatar.

KU KARANTA: Biden ya cire dokar da ta hana mutanen wasu kasashe shigowa Amurka

A matsayinta na mukaddashiyar Darekta, Ebong za ta jagoranci USTDA wajen hulda da ‘yan kasuwa masu zaman kansu domin inganta tattalin Amurka.

Haka zalika daga cikin aikin da ke gaban Miss Ebong shi ne ta taimakawa gwamnatin Amurka wajen fitar da kaya daga kasar zuwa kasashen ketare.

Kafin dawowar ta wannan hukuma ta kasuwancin tarayya, Ebong ta rike kujera mai tsoka a cibiyar da ake kira Milken Center for Advancing the American Dream.

A cibiyar, Ebong ta yi kokari wajen habakka sha’anin kiwon lafiya, ilmi, kasuwanci da neman na kai.

Joe Biden ya nada Enoh Ebong ta rike Hukumar USTDA na rikon kwarya
Enoh T. Ebong Hoto: Twitter Daga: @Naija_PR
Asali: Twitter

KU KARANTA: Janar Olonisakin ya yi ban-kwana da khaki, ya tare a gida

Da ake rantsar da ita a matsayin shugabar riko, Ebong ta ce ta ji dadin dawowar ta USTDA. Ebong ta yi karatu a jami’o’in Michigan, Pennsylvania, da Edinburgh.

A baya kun ji cewa wata 'yar Najeriya ta samu daukaka a gwamnatin Amurka inda Joe Biden ya nada Funmi Olorunnipa Badejo a matsayin mai ba da shawara.

Kafin nan 'dan Najeriya Adewale Adeyemo ya zama mataimakin ministan asusun Amurka.

Funmi mai auren wani 'dan Najeriya Tunde Badejo, ta fito ne daga jihar Kogi, kuma ta kasance tsohuwar dalibar makarantar Berkeley Law College ta Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng