Biden zai yi karin kumallo da dokar da Trump ya kakabawa kasashen Musulmai

Biden zai yi karin kumallo da dokar da Trump ya kakabawa kasashen Musulmai

- Joe Biden zai cire dokar da ta hana mutanen wasu kasashe shigowa Amurka

- A ranar da aka rantsar da Joe Biden, za a fara rusa manufofin Donald Trump

- Ana sa ran kasashe musamman na musulmi zasu sake samun damar sararawa

A ranar farko da zai yi a ofis, zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya na shirin daukar matakan da zasu yi fatali da wasu manufofin Donald Trump.

Rahotanni daga Aljazeera sun tabbatar da cewa Joe Biden zai sa hannu a dokoki har da wanda zai soke takunkumin da aka sa a kan wasu kasashe na musulmai.

Wata takarda da ta fara yawo a ranar Asabar ta nuna cewa dokar da Donald Trump ya kakaba wa wadannan kasashe ba za ta kwana a gwamnatin Joe Biden ba.

Takardar ta fito ne daga hannun Ron Klain, wanda zai rike kujerar shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Amurka a karkashin mulkin shugaban kasa Biden.

KU KARANTA: Coge aka yi a zaben 2020, ina da hujjoji - Trump

Ron Klain ya bayyana cewa shugaban kasa mai jiran-gado Joe Biden, zai soke wasu manufofin gwamnatin Donald Trump da zarar ya shiga ofis a ranar Laraba.

Kamar yadda Klain ya bayyana, Biden zai yi wannan ne a kwanakin goman farko da zai yi a ofis.

A ranar da aka rantsar da Biden, zai bada sanarwar dakatar da dokar da Donald Trump ya kawo na hana wasu kasashe masu yawan musulmai, shigowa cikin Amurka.

Sauran sauyin da Biden zai kawo cikin gaggawa sun hada da maida Amurka cikin yarjejeniyar sauyin yanayi da Paris, wanda gwamnatin Trump ta fitar da kasar.

KU KARANTA: Wacece Matar da ta tsige Shugaba Donald Trump sau biyu a Amurka

Biden zai yi karin kumallo da dokar da Trump ya kakabawa kasashen Musulmai
Joe Biden Hoto: www.afp.com/en
Source: UGC

Bayan haka, Biden zai ba miliyoyin mutanen kasar waje damar samun takardar zama ‘yan Amurka.

A makon jiya kun ji cewa Donald Trump yanzu ya zama shugaban Amurka na farko a tarihi da majalisar tarayya ta tsige sau biyu daga kan kujerar shugaban kasa.

A kuri'un da 'yan majalisar wakilan suka kada, har 'yan jam'iyyarsa sun goyi bayan a tsige shi.

Rahotanni sun bayyana cewa idan majalisar dattawa ta amince a kori Donald Trump daga ofis, ba zai sake iya takarar kujeran shugaban kasa a Amurka ba har abada.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel