Tsohon Shugaban hafsun sojoji, Janar Olonisakin ya samu kyakkyawar tarba a gida

Tsohon Shugaban hafsun sojoji, Janar Olonisakin ya samu kyakkyawar tarba a gida

- Abayomi Gabriel Olonisakin ya koma gidansa bayan ya yi ritaya daga aikin soja

- ‘Yanuwa da abokan arziki sun tarbi Janar Gabriel Olonisakin (mai ritaya) a gida

- An shirya biki ga tsohon Hafsun Sojojin Kasar da ya shafe shekaru 40 ya na aiki

Bayan tsawon shekara da shekaru ya na aiki a gidan soja, Abayomi Gabriel Olonisakin, ya yi ritaya, ya koma gidansa a makon da ya gabata.

Wani faifan bidiyo ya nuna sa’ilin da Janar Gabriel Olonisakin ya isa gida, ya hadu da iyalinsa.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ana ta yawo da wannan bidiyo na tsohon shugaban hafsun sojojin na Najeriya a dandalin sada zumunta na Twitter.

Kamar yada wannan bidiyo da Deji Adesogan ya fito da shi ya nuna, za a ga tsohon sojan ya na rungume uwargidarsa bayan ya fito daga motarsa.

KU KARANTA: Za a yi wa manyan Jami’an Sojoji akalla 20 ritaya a gidan soja

Haka zalika tsohon hafsun kasar, Abayomi Gabriel Olonisakin ya hadu da sauran ‘yanuwa da abokan arzikin da su ka zo taya shi murnar kammala aiki.

Janar Gabriel Olonisakin wanda ya shiga gidan soja a shekarar 1981, ya shafe tsawon shekaru biyar da rabi a kan kujerar shugaban hafsun sojoji na kasa.

Za a ji jama’a su na ta yi wa Janar Olonisakin (mai ritaya) wake-wake, ana ta busa sarewa domin a na nuna godiya ga Ubangiji da yi wa 'dan na su san-barka.

Olonisakin ya cire hularsa domin ya karbi gaisuwar da ake yi masa, sannan ya shiga tika rawa tare da sauran ‘yanuwa da iyalin gidansa da ke ta faman murna.

KU KARANTA: Babu Jami’in kabilar Ibo a jerin sababbin hafsun Sojoji

Tsohon Shugaban hafsun sojoji, Janar Olonisakin ya samu kyakkyawar tarba a gida
Janar Abayomi Gabriel Olonisakin Hoto: Defence Info
Asali: Twitter

Za a iya ganin Janar Olonisakin mai ritaya ya na daga hannuwansa yayin da busar da ake yi ta ke kara karfi, shi kuma ya na gefe guda ya rawa da sauran jama’a.

Gabriel Olonisakin sun yi ritaya ne a makon da ya wuce, bayan mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wasu sababbin hafsun sojoji.

Shugaban kasar ya maye gurabensu da Manjo Janar Leo Irabor, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, Rear Admiral Auwal Zubairu Gambo Air Vice Marshal IO Amao.

Gabriel Olonisakin da takwaorinsa, su na cikin hafsun sojojin da su ka fi kowane dadewa a tarihi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel