Joe Biden ya ba wata ƴar Nigeria muƙami a sabuwar gwamnatinsa

Joe Biden ya ba wata ƴar Nigeria muƙami a sabuwar gwamnatinsa

- Wata yar Najeriya ta sake daukaka martabar kasar a Amurka

- Hakan na zuwa ne yayinda Joe Biden ya nada Funmi Olorunnipa Badejo a matsayin mai ba da shawara

- Lauyar wacce ta ke haifaffiyar yar Najeriyar ta kasance tsohuwar dalibar Berkeley Law College

Yan makonni bayan ambatan dan Najeriya Adewale Adeyemo a matsayin mataimakin ministan asusun Amurka, zababben shugaban kasar Amurka Joe Biden ya nada haifaffiyar yar Najeriya Funmi Badejo a matsayin daya daga cikin masu bashi shawara kan doka a fadar White House.

An nada Olorunni Badejo a matsayin mai bayar da shawara yayinda tsohon mataimakin shugaban kasar ya ambaci fiye da lauyoyi 20 a matsayin hadimansa na fadar White House a ranar Talata, 12 ga watan Janairu, Bloomberg Law ta ruwaito.

Daga cikin mutanen da aka ambata cikin tawagar lauyoyin Biden na White House harda Samiyyah Ali wacce aka nada a matsayin mataimakiyar abokiyar shawara.

Joe Biden ya ba wata ƴar Nigeria muƙami a sabuwar gwamnatinsa
Joe Biden ya ba wata ƴar Nigeria muƙami a sabuwar gwamnatinsa Hoto: @BerkeleyLawCDO, Zola
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta sake rashin AIG na biyu cikin kwanaki 3

Sai Tona Boyd a matsayin abokiyar shawara na musamman da Megan Ceronsky a matsayin abokiyar shawara.

Funmi, wacce ke auren wani dan Najeriya Tunde Badejo, ta fito daga jihar Kogi, kuma ta kasance tsohuwar dalibar makarantar Berkeley Law College a kasar Amurka.

Funmi wacce ta kasance yar wata bakuwar haure da ta nemi a kira ta da Florida, ta kasance babbar mai bayar da shawara a karamin kwamitin majalisa kan annobar korona.

Ta kammala jami’ar California, Berkeley, makarantar lauyoyi, jami’ar Harvard, da jami’ar Florida.

Olorunnipa Badejo na zama a Washington D.C. tare da mijinta da danta, kamar yadda bayaninta a shafin yanar gizo kan mika mulki na Biden-Harris ya nuna.

KU KARANTA KUMA: Abdulmumuni Ningi: Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar Bauchi

A wani labarin, a ranar Laraba, 13 ga watan Janairu, majalisar wakilan Amurka ta kafa tarihi yayinda ta tsige Shugaban kasa Donald Trump, karo na biyu a zango daya.

An tsige shugaban kasar Amurkan bayan ya zuga mabiyansa don su kai hari Capitol a kokarinsa na hana tabbatar da nasarar zababben Shugaban kasa Joe Biden.

Majalisar ta jefa kuri’u 232 cikin 197 don tsige Shugaban kasar. Sai dai, sabanin tsigewar farkon, yan jam’iyyar Republican 10 sun hade da yan Democrats wajen tsige shugaban kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel