Korona: Ku yi allurar rigakafi ko ku mutu, FG ta gargadi yan Nigeria

Korona: Ku yi allurar rigakafi ko ku mutu, FG ta gargadi yan Nigeria

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa allurar rigafin COVID-19 ce kawai mafita don shawo kan cutar

- Harma, Shugaban kwamitin PTF, Boss Mustapha, ya bayyana cewa yan Najeriya da dama na iya mutuwa idan ba rigakafin

- Mustapha ya kuma bayyana cewa kasashe a fadin duniya za su fara bukatar shaidar yin rigakafin kafin su ba matafiya damar shiga cikinsu

Akwai gagarumin hatsari cewa yan Najeriya da dama na iya kamuwa da rashin lafiya da kuma mutuwa idan suka yi watsi da allurar rigakafin COVID-19.

Boss Mustapha, Shugaban kwamitin fadar Shugaban kasa kan korona (PTF) kuma babban sakataren tarayya ne ya sanar da wannan fargabar a ranar Talata, 2 ga watan Fabrairu a yayin wani taro a Abuja, PM News ta ruwaito.

Mustapha ya bayyana cewa rigakafin da ake magana a kai bai da illa kuma zai amfani al’umma sosai yayinda suke kokarin shawo kan annobar ta duniya sannan yayi watsi da ikirarin cewa an samar da rigakafin ne don kashe yan Afrika.

Korona: Ku yi allurar rigakafi ko ku mutu, FG ta gargadi yan Nigeria
Korona: Ku yi allurar rigakafi ko ku mutu, FG ta gargadi yan Nigeria Hoto: @DigiCommsNG
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Tsohuwar da bata samu haihuwa ba ta ce ita da kanta ta nema wa mijinta sabuwar mata

Hakazalika, Shugaban na PTF ya bayyana cewa kwanan nan za a fara bukatar shaidar yin rigakafin kafin a bari mutane su yi tafiya da kuma amincewa da shigarsu kasashe.

“Za mu roki mutanenmu tare da yi musu bayanin cewa idan ba ku yi rigakafin ba, akwai gagarumin hatsarin fadawa hali na rashin lafiya da kuma yiwuwar mutuwa a nan.

“Za mu fada masu cewa idan ba ka yi rigakafin COVID-19 ba, ba lallai ne ka samu zuwa ko ina ba a duniya, nan kusa. Koda kuwa kana so ka je sauke farali, wannan zai ta’allaka ne kan sanin matsayin koronan ka.”

KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye: Kasashe 44 da yan Najeriya za su iya zuwa ba tare da biza ba

A gefe guda, mun ji cewa a yanzu sanya takunkumin fuska a wuraren jama’a a Najeriya ya zama wajibi kamar yadda dokar kariya daga annobar korona ta 2021 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a ranar 26 ga watan Janairu ya nuna.

Sakamakon haka, Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya umurci jami’ansa da su tabbatar da bin tsarin, Legit.ng ta ruwaito.

Da wannan, duk wanda yaki bin umurnin ko yaki sauraron jami’an da ke tursasa dokar na iya fuskantar kamu da hukunci a kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel