Hanya mafi sauki don magance rikicin makiyaya, Mataimakin gwamnan Benue

Hanya mafi sauki don magance rikicin makiyaya, Mataimakin gwamnan Benue

- Mataimakin gwamnan jihar Benue ya bai wa gwamnonin jihohin Ondo, Oyo da sauransu shawara kan makiyaya

- Ya bayyana musu hanyar da ya kamata su bi don magance rikici tsakanin fulani makiyaya da manoma

- Mataimakin gwamnan ya jaddada shawararsa cewa tana aiki sosai a jihar Benue, kuma an samu zaman lafiya

Mataimakin gwamnan jihar Benue, Benson Abounu, ya shawarci Ondo, Oyo da sauran jihohin da ke fama da rikicin makiyaya a kasar nan da su yi la’akari da kafa dokar hana kiwo a fili irin na jihar Benue, The Punch ta ruwaito.

Jihohin Oyo da Ondo sun kasance cikin guguwar kwanan nan dangane da kalubalen tsaro da kuma kokarin kula da zirga-zirgar makiyaya.

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce jihar ta kafa dokar hana kiwo a fili amma ya ce akwai kalubale wajen aiwatar da dokar.

KU KARANTA: Dalilin da yasa ba a damawa da Matan Arewa a fannin da ya shafi fasaha

Hanya mafi sauki don magance rikicin makiyaya, Mataimakin gwamnan Benue
Hanya mafi sauki don magance rikicin makiyaya, Mataimakin gwamnan Benue Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Gwamnan ya kara da cewa hadin kan ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na tarayya na da matukar mahimmanci wajen aiwatar da dokar da aka kafa domin dakatar da yawan rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Amma mataimakin gwamnan Benue ya ce dokar na aiki sosai a jihar. Ya yaba wa rundunar ‘yan sanda ta Jihar Benuwai kan kyakkyawan aikin da suka yi wajen aiwatar da dokar hana kiwo a fili a jihar.

Ya kuma ce gwamnatin jihar ta kame shanu 356 da makiyaya shida dauke da makamai kwanan nan kuma an mika masu laifin da shanunsu ga ‘yan sanda don gurfanar da su.

Abounu ya ce, “’Yan sanda a Benue sun yi kyakkyawan aiki musamman wajen kiyaye dokarmu ta hana kiwo a fili.

"Adadin da yawa (na masu laifi) an kama su a baya kuma an yi musu shari'a daidai da laifinsu. Wasu daga cikinsu an yanke musu hukunci a cibiyoyin gyara yayin da wasu suka biya tara."

Mataimakin gwamnan ya kuma lura cewa gwamnatin jihar ba ta adawa da kiwon shanu, ya kara da cewa a koyaushe tana ba makiyaya a jihar shawarar su rungumi tsarin kiwon.

KU KARANTA: Zan bar aiki cikin farin ciki domin na cika burina, tsohon hafsin sojin sama

A wani labarin, Gwamnatin Ogun a ranar Litinin ta karyata rahotannin da ke nuna cewa ta nemi taimakon Sunday Adeyemo, da aka fi sani da Sunday Igboho, don magance laifuka a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar, Abdulwaheed Odusile, ya yi watsi da rahoton a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta sa’o’i bayan Igboho ya isa jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.