Abubuwa 4 da Shugaban ma’aikatan tsaro ya fada ma dakarun da ke fagen fama a Maiduguri

Abubuwa 4 da Shugaban ma’aikatan tsaro ya fada ma dakarun da ke fagen fama a Maiduguri

- Sabbin shugabannin tsaro sun ziyarci jihar Borno a ranar Lahadi, 31 ga watan Janairu

- Karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan tsaro, CDS, Janar Lucky Irabor, ana sanya ran ziyarar nasu zai kawo gagarumin nasara kan yan ta’addan Boko Haram

- CDS din ya kuma jadadda wasu batutuwa yayinda yake jawabi ga dakarun da ke filin daga a Maiduguri, jihar Borno

Tuni sabon shugaban ma’aikatan tsaro, CDS, Janar Lucky Irabor, ya fara zantuka masu tsauri.

Da yake magana a yayinda shugabannin tsaro suka ziyarci Maiduguri, babbar birnin jihar Borno kwanan nan, Janar Irabor ya sake jadadda wasu zantuka ga dakarun da ke fagen fama.

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole a mika shugabancin kasa zuwa kudu a 2023, Sanata Gaya

Abubuwa 4 da Shugaban ma’aikatan tsaro ya fada ma dakarun da ke fagen fama a Maiduguri
Abubuwa 4 da Shugaban ma’aikatan tsaro ya fada ma dakarun da ke fagen fama a Maiduguri Hoto: @ProfZulum
Asali: Twitter

Ga wasu manyan zantuka daga jawabin shugaban ma’aikatan tsaron a yayin ziyarar a kasa:

1. Shugaban kasa, babban kwamanda ya aiko sakon jinjinarsa zuwa gare ku. Da muka hadu da shi, ya bukacemu da mu bari ku san cewa jin dadinku na da matukar muhimmanci a gwamnati sannan mu bari ku san cewa gwamnati na aiki kan lamarin da ya shafi karin kayayyakin aiki a kan wanda aka siyo da wadanda ke hanyar zuwa Najeriya.

2. Za ku dunga ganinmu akai-akai, domin ku san cewa muna tare da ku da kuma tabbatar da ganin cewa wannan aikin ya zo karshe cikin sauri.

KU KARANTA KUMA: A kula: Yan sanda na iya kama ka a wajen taron jama’a daga ranar 2 ga watan Fabrairu

3. Duk wani shugaban tsaro da ni kaina mun amince cewa za mu yi duk abunda ake bukata daga garemu don aiki a matsayin tawaga guda

4. Sannunku da kokari, ku ci gaba da jajircewa don hakan ne ya kamata. Bamu da wani zabi illa mu cika muradan babban kwamandanmu.

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon shugaban rundunar sojojin sama na Najeriya ya bayyana farin cikinsa na barin aiki.

Ya bayyana cewa, ya cimma burinsa na abindsa yake son cimmawa a aikin soja.

Hakazalika ya karfafi gwiwa hade da godiya da rundunar sojin sama da yayi aiki dasu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng