Ya zama dole a mika shugabancin kasa zuwa kudu a 2023, Sanata Gaya
- Sanata Kabiru Gaya ya nuna muradinsa na son ganin yankin kudu ya samar da shugaban kasa na gaba
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce shine abunda ya kamata ayi ta bangaren hade kan kasar
- Ya yi kira ga yan siyasa da su mutunta tsarin mulkin karba-karba don ra'ayin kasar
Sanata Kabiru Gaya ya bayyana cewa ya kamata yankin Kudancin Najeriya ya samar da shugaban kasa na gaba a 2023 don yin adalci.
Gaya ya fadi hakan ne yayinda yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Abuja kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.
Ya bayyana cewa Arewa ta samar da shugaban kasa na tsawon zango biyu wato shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a cewarsa yayi namijin kokari wajen ci gaban kasar.
KU KARANTA KUMA: Edo: Yan majalisa 2 sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP
A cewar sanatan, shugaban kasa Buhari na iya bakin kokarinsa a kan kasar.
“Kan lamarin shugabancin kasa a 2023, zan marawa shugaban kasa daga yankin Kudancin kasar baya. Lokaci yayi da ya kamata mu samu shugaban kasa daga yankin kudu yayinda Mataimakin shugaban kasa zai fito daga arewa.
“Ina ganin ya kamata ayi adalci wajen juya shugabanci ta yadda mutane za su yi amanna da tsarin; daga arewa har kudu za su rungumi junansu. Akwai bukatar Najeriya ya zama kasa daya. Kasa daya mai hadin kai,” in ji shi.
Kan kira ga sauya fasalin lamura, Gaya ya bayyana cewa ya kamata Najeriya ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa daya yayinda take inganta hanyar tattara kudaden shigarta.
“Allah ya san abunda yafi shiyasa ya sa mu a waje guda kuma nayi imani akwai dalilin hakan.
“Amma idan kace kana so ka sauya fasalin lamuran kasar ta hanyar amfani da kudaden shiga, cewa kowace jiha ta ci gashin kanta ko yankunan kasar suyi ta kansu, Ina ganin wannan ne tunanin wasu yan Najeriya.
KU KARANTA KUMA: A kula: Yan sanda na iya kama ka a wajen taron jama’a daga ranar 2 ga watan Fabrairu
“Ina ganin cewa ya kamata Najeriya ta ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya,” in ji shi.
Dan majalisar ya nuna bukatar cewa ya kamata Najeriya tayi amfani da albarkatunta don ci gaban kasar.
A gefe guda, wani fitaccen masanin kimiyyar magunguna kuma tsohon shugaban kwamitin kungiyar tattalin arziki na Nigeria, Sam Ohuabunwa ya sanar da niyyarsa na fitowa takarar shugaban kasa kasa a 2023.
Shine shugaban kungiyar masana kimiyyar magunguna ta Nigeria, Pharmaceutical Society of Nigeria, PSN.
Mista Ohuabunwa kwararre ne da ba a san shi da shiga harkokin siyasa a Nigeria ba a baya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng