Zan bar aiki cikin farin ciki domin na cika burina, tsohon hafsin sojin sama
- Tsohon shugaban rundunar sojojin sama na Najeriya ya bayyana farin cikinsa na barin aiki
- Ya bayyana cewa, ya cimma burinsa na abindsa yake son cimmawa a aikin soja
- Hakazalika ya karfafi gwiwa hade da godiya da rundunar sojin sama da yayi aiki dasu
Shugaban hafsan sojan sama mai barin gado, Air Marshall Sadique Abubakar, a ranar Talata, ya ce zai bar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) cikin farin ciki, saboda ya cika duk wasu manufofin sa na aikin, The Nation ta ruwaito.
Sadique wanda ya yi magana a lokacin da yake gudanar da faretin tashi daga filin jirgin saman NAF da ke Abuja, ya ce a cikin shekaru biyar da suka gabata, an sake dawo da martabar rundunar sojojin sama ta Najeriya ta zama “kwararriya kuma mai ladabi."
A cewarsa, “Na gode wa Allah da Ya ba ni dama ta musamman ta kasancewa a shugabancin harkokin rundunar Sojin sama tun 13 ga watan Yulin, 2015,
KU KARANTA: Bamu gayyaci Sunday Igboho ya ya taya mu korar Fulani ba, gwamnan jihar Ogun
"Ina yi masa godiya kan taimako da kariya da ya ba ni a lokacin da nake Shugaban Hafsun Sojojin Sama da ba ni damar samun nasarar fita daga aiki kasancewar na rike matsayin Babban hafsan sojojin sama na 20 tsawon shekaru 5, watanni 6 da kwanaki 13."
Sadique ya bayyana jin dadinsa da jinjinawa ga rundunarsa ta sojin sama a matsayin tawaga mai kishin kasa.
"Tutar rundunar sojin saman Najeriya a yau tana daga sama daga Agatu zuwa Gembu zuwa Gusau zuwa Katsina zuwa Daura zuwa Owerri zuwa Birin Gwari, Ipetu Ijesha, Kerang, Gombe da Bauchi.
"Da yardar Allah na musamman Funtua nan bada jimawa ba zata haɗu. Tsarin da yake gudana a yanzu tabbas zai kara wa ma'aikatar NAF kima sosai a kokarin da take na tabbatar da Najeriya da kuma mutanen Najeriya ”.
A karshe yana mai cewa,“Yayin da na bar rundunar sojan sama ta Najeriya, zan bar aikin cikin cika buri saboda na samu nasarar abin da na sa a gaba. Ina son in gode wa dukkan danginmu musamman mahaifiyata tsohuwa kan goyon baya da addu’a da fahimta da suka ba ni.”
KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Borno zata kafa kwalejin ilimin addinin Musulunci guda 27
A wani labarin, Sabbin hafsoshin sojan Najeriya sun isa Maiduguri, babban birnin jihar Borno tare da niyyar ganawa da masu ruwa da tsaki don shawo kan yadda za a magance tayar da kayar baya a fagen daga.
Babban hafsan hafsoshin tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ya jagoranci shugabannin hafsoshin zuwa hedikwatar rundunar tsaro ta rundunar Operation Lafiya Dole da ke Maiduguri da misalin karfe 1:30 na rana a ranar Lahadi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng