A kula: Yan sanda na iya kama ka a wajen taron jama’a daga ranar 2 ga watan Fabrairu

A kula: Yan sanda na iya kama ka a wajen taron jama’a daga ranar 2 ga watan Fabrairu

- An ba jami’an yan sanda izinin kama duk wani dan Najeriya da yaki sanya takunkumin fuska a taron jama’a

- Hakan ya biyo bayan sanya hannu a dokar kula da kare kai da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a ranar 26 ga watan Janairu

- Har ila yau, tsarin ya hana taro a wuraren jama’a

A yanzu sanya takunkumin fuska a wuraren jama’a a Najeriya ya zama wajibi kamar yadda dokar kariya daga annobar korona ta 2021 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a ranar 26 ga watan Janairu ya nuna.

Sakamakon haka, Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya umurci jami’ansa da su tabbatar da bin tsarin, Legit.ng ta ruwaito.

Da wannan, duk wanda yaki bin umurnin ko yaki sauraron jami’an da ke tursasa dokar na iya fuskantar kamu da hukunci a kotu.

KU KARANTA KUMA: Jerin manyan jami’an yan sanda da ka iya maye gurbin Adamu a matsayin IGP

A kula: Yan sanda na iya kama ka a wajen taron jama’a daga ranar 2 ga watan Fabrairu
A kula: Yan sanda na iya kama ka a wajen taron jama’a daga ranar 2 ga watan Fabrairu Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Bugu da kari, laifin na da hukuncinsa a karkashin doka, inda za a ci tarar mutum ko kuma zama a gidan kurkuku na watanni shida ko ma dukka hukuncin biyu kamar yadda yake a sashi na 5 na dokar Killace kai.

Tsarin ya kuma sanya haramci kan taro a wuraren jama’a- wuraren bauta, wurin aiki da makarantu, bankuna, motocin haya, dakunan kwanan dalibai, makarantun kwana, cibiyoyin tsare mutane.

KU KARANTA KUMA: Ku hankalta! Jerin jihohi 5 da kananan hukumomi 22 da FG ta ce cutar korona ta yadu sosai

A wani labarin, mun ji cewa wata kotun tafi da gidanka a Abuja ta bada umarnin rufe kasuwar Wuse da ke Zone 5 saboda take dokokin dakile yaduwar cutar korona a kasuwar, The Cable ta wallafa hakan.

An rufe kasuwar UTC da rukunin shagunan Murg da ke yanki na 10 a Garki duk bayan umarnin kotun.

Kwamitin tabbatar da bin dokar korona ta Abuja wacce ta ziyarci kasuwar a ranar Litinin ta bayyana yadda ta samu babu na'urar gwada dumin jiki, ba a amfani da takunkumin fuska da kuma abubuwan wanke hannu a kasuwar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng