'Yan bindiga sun sace mahaifin shugaban wata karamar hukuma a Abuja

'Yan bindiga sun sace mahaifin shugaban wata karamar hukuma a Abuja

- Yan bindiga sun sace mahaifin wani shugaban karamar hukuma a babban birinin tarayya

- Bayan harbin iska da suka yi a gidan mahaifin, sun tafi dashi tare da wasu mutanen gidan

- 'Yan bindigan sun bar lambar waya da za a iya samunsu domin biyan kudin fansa

'Yan sanda a Abuja a ranar Talata, sun tabbatar da sace Mista John Makama, mahaifin Shugaban Karamar Hukumar Bwari, John Gabaya, The Nation ta ruwaito.

CSP Biodun Makanjuola, jami’in ‘yan sanda na shiyya (DPO), mai kula da ofishin 'yan sanda na Bwari, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN).

Makanjuola ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na rana a ranar Talata, ya kara da cewa ‘yan sanda na tattara bayanai kan hakikanin abin da ya faru.

KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Borno zata kafa kwalejin ilimin addinin Musulunci guda 27

'Yan bindiga sun sace mahaifin shugaban karamar hukumar Bwari -' yan sanda
'Yan bindiga sun sace mahaifin shugaban karamar hukumar Bwari -' yan sanda Hoto: eNCA
Source: UGC

Ya ce an yi garkuwa da mahaifin nasa tare da wasu 'yan uwansa biyu, ya kara da cewa 'yan sanda suna dabarun kubutar da su ba tare da sun ji rauni ba.

Wani dan gidan Makama da ya so a sakaya sunansa ya fada wa NAN, cewa ’yan bindigar sun kutsa kai gidan mahaifin shugaban karamar hukumar inda suka yi ta harbi a iska lokaci zuwa lokaci.

Majiyar ta ce da farko ‘yan bindigar sun kame Makama, matarsa, da ake kira “ Mama ’’, da wasu mutum biyu, amma sun saki Mama bayan da mijinta ya roki su sake ta.

A cewar majiyar, masu garkuwan sun bar lambar wayar da za same su kuma tuni sun nemi a biya su kudin fansa kafin a sako wadanda aka yi garkuwar da su.

KU KARANTA: Bamu gayyaci Sunday Igboho ya ya taya mu korar Fulani ba, gwamnan jihar Ogun

A wani labarin, Wani farmaki da wasu jami'an 'yan sanda, 'yan banga da mafarauta a jihar Adamawa suka kai wa mambobin kungiyar 'yan fashi ya yi sanadiyyar kashe biyu daga cikin 'yan fashin tare da kame daya.

Sauran mambobin kungiyar sun tsere bayan an ci karfinsu a farmakin, wanda ya faru da sanyin safiyar Litinin a kusa da karshen Numan na Babbar Hanyar Numan zuwa Jalingo, The Nation ta ruwaito.

DSP Suleiman Nguroje a jihar ta Adamawa, ya ce a cikin wata sanarwa da safiyar Litinin din da ta gabata an fara gudanar da aikin tsaro cikin nasara bisa umarnin kwamishinan 'yan sanda, CP Aliyu Adamu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel