Edo: Yan majalisa 2 sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP

Edo: Yan majalisa 2 sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP

- Wasu mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) biyu sun sauya sheka zuwa Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar dokokin jihar Edo

- Yan majalisar sune Yekini Idaiye mai wakiltan Akoko-Edo 1 da Nosayaba Okunbor mai wakiltan Orhionmwon East

- San daura alhakin sauya shekar nasu a kan rabuwar kan da ke APC a kananan hukumominsu

Yan majalisar dokokin jihar Edo guda biyu wadanda suka kasance mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a jiya Litinin, 1 ga watan Fabrairu sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Yan majalisar sun bayyana cewa sun sauya sheka ne sakamakon rabuwar kai da ke a jam’iyyar APC a kananan hukumominsu.

Bayan sauya shekar nasu, a yanzu jam’iyyar PDP na da mambobi tara yayinda APC ke mutum daya a majalisar dokokin jihar mai kunshe da mutum 10, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Edo: Yan majalisa 2 sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP
Edo: Yan majalisa 2 sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: A kula: Yan sanda na iya kama ka a wajen taron jama’a daga ranar 2 ga watan Fabrairu

Kakakin majalisar dokokin jihar, Marcus Onubu, ne ya karanto wasikun sauya shekar yan majalisar; Yekini Idaiye (Akoko-Edo 1) da Nosayaba Okunbor (Orhionmwon East).

Kakakin majalisar ya kuma yi masu maraba da zuwa PDP sannan ya jinjina masu a kan kudirinsu na yin aiki tare da gwamnan jihar wajen ci gaban jihar.

A wani labari na daban, mun ji cewa mai tsawatarwa a Majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya dira babban kotun tarayya dake Abuja don gurfanar da shi kan zargin almundahanar biliyan 7 kudin jihar Abia da yayi yana gwamna.

Tsohon gwamnan na gurfana gaban, Alkali Inyang Ekwo, ranar Talata, 2 ga Febrairu, 2021.

KU KARANTA KUMA: Jerin manyan jami’an yan sanda da ka iya maye gurbin Adamu a matsayin IGP

Za ku tuna cewa an kama Orji Uzor Kalu, wanda yayi gwamnan jihar Abia daga 1999 zuwa 2007, da laifin almundahana kuma aka jefa shi kurkukun shekara 12.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng