Jerin manyan jami’an yan sanda da ka iya maye gurbin Adamu a matsayin IGP

Jerin manyan jami’an yan sanda da ka iya maye gurbin Adamu a matsayin IGP

Yan Najeriya na nan sun zuba idanu don ganin wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai nada a matsayin sufeto janar na yan sanda yayinda Mohammed Adamu, IGP mai ci ya kai shekarun yin ritaya, bayan ya shafe tsawon shekaru 35 a hukumar.

Jaridar Daily Trust a wani sabon rohoto ta jero wasu manyan jami’an yan sanda da ka iya darewa babban kujerar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari garuruwan Niger, sun kashe mutum 21 tare da garkuwa da wasu 40

Jerin manyan jami’an yan sanda da ka iya maye gurbin Adamu a matsayin IGP
Jerin manyan jami’an yan sanda da ka iya maye gurbin Adamu a matsayin IGP Hoto: Femi Adesina
Source: Facebook

Mataimakan Sufeto Janar na yan sanda (DIGs)

Wa’adin shugabancin IGP bisa kundin tsarin mulki shekaru hudu ne tare da zango daya na sabonta shi. Sai dai, Daily Trust ta lura cewa babu ko mutum daya cikin masu mukamin DIG da ke da sauran shekaru hudu kafin ritaya.

Hakan na nufin idan aka nada su mukamin, ba za su iya kammala cikakken wa’adi a matsayin IGP ba.

KU KARANTA KUMA: Ku hankalta! Jerin jihohi 5 da kananan hukumomi 22 da FG ta ce cutar korona ta yadu sosai

DIGs da ke da sauran lokaci.

1. Dan-Mallam Mohammed

2. Usman Alkali Baba

3. Sanusi Lemu

Dukkansu manyan jami’an yan sandan uku za su bar aiki a 2023.

AIG da ka iya hawa matsayin

Daily Trust a bincikenta ta bayyana cewa mutum uku cikin AIGs masu ci na da sauran shekaru hudu a aiki.

Yayinda biyu daga cikinsu za su yi ritaya a 2025, dayan na da sauran shekaru tara kafin yayi ritaya.

1. Dasuki Danbappa Galadanchi

2. Hafiz Mohammed Inuwa

AIG da ke da mafi yawan shekarun aiki da yayi masa saura

1. Moses Ambakina Jitoboh (AIG da ke kula da fatrol a iyaka)

An tattaro cewa wasu manyan masu fada aji ciki harda tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan sun shige ma takarar Jitoboh gaba.

Babban dan sandan ya kasance dan jihar Bayelsa.

Manyan jami’an da ke jayayyar amma basu da shekaru hudu

1. AIG Dan-Mallam Mohammed

2. AIG Zanna Ibrahim

AIGs da ke da kasa da shekaru hudu a aiki amma kuma suke takarar kujerar

1. Zanna Ibrahim

2. Mustapha Dandaura

3. Garba Baba Umar

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel