Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari garuruwan Niger, sun kashe mutum 21 tare da garkuwa da wasu 40

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari garuruwan Niger, sun kashe mutum 21 tare da garkuwa da wasu 40

- Yan bindiga sun kai farmaki wasu garuruwa a karamr hukumar Shiroro da ke jihar Niger

- Harin wanda ya afku a ranar Talata, ya yi sanadiyar halaka mutane 21 yayinda aka yi garkuwa da wasu 40

- Sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Matane ya tabbatar da afkuwar lamarin

Rahotanni sun kawo cewa an kashe mutane 21 sannan aka yi garkuwa da wasu 40 a wani sabon hari da yan bindiga suka kai kan garuruwan Shiroro a jihar Niger.

Hare-haren sun afku ne a safiyar ranar Talata lokacin da kimanin yan bindiga 300 kan babura suka farma garuruwan Kurege, Sabon Gida, Sararai da Rafin Kanya inda suka yi ta harbi ba kakkautawa, jaridar Punch ta ruwaito.

Wani idon shaida wanda ya kuma kasance dan asalin karamar hukumar Shiroro, Galadima Salisu yayinda yake tabbatar da lamarin, ya fada wa manema labarai a wayar tarho cewa yana tsoron cewa yan bindiga da ke cin karensu ba babbaka za su iya karbe su.

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari garuruwan Niger, sun kashe mutum 21 tare da garkuwa da wasu 40
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari garuruwan Niger, sun kashe mutum 21 tare da garkuwa da wasu 40 Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Salisu ya ce za a hana faruwar hakan ne kadai idan gwamnati a dukkan matakai suka kawo masu agaji.

KU KARANTA KUMA: Ku hankalta! Jerin jihohi 5 da kananan hukumomi 22 da FG ta ce cutar korona ta yadu sosai

Duk wani kokari na tuntubar jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun, don jin ta bakin shi kan lamarin ya ci tura.

Da aka tuntube shi kan wayar tarho, sakataren gwamnatin jihar Niger, Ahmed Ibrahim Matane ya tabbatar da lamarin. Sai dai ya karyata samun masaniya a kan yawan mutanen da aka kashe.

Matane ya jadadda cewa gwamnatin jihar Niger na yin iya bakin kokarinta don magance matsalar rashin tsaro da ke addabar mutanenta.

Yan bindiga a jihar Niger sun kara yawan hare-harensu kan jihar tun bayan bayyanar labarin nadin sabbin shugabannin tsaro da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: FG ta ƙara wa'adin haɗa lambar NIN da layin waya zuwa 6 ga watan Afrilu 2021

A wani labarin, mun ji cewa yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane da dama a kauyen Garawa, karamar hukumar Giwa jihar Kaduna.

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan da rundunar sojin sama ta samu nasarar kakkabe wasu yan bindiga a garuruwan Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun.

Kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida, Mr Samuel Aruwan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng