Ku hankalta! Jerin jihohi 5 da kananan hukumomi 22 da FG ta ce cutar korona ta yadu sosai

Ku hankalta! Jerin jihohi 5 da kananan hukumomi 22 da FG ta ce cutar korona ta yadu sosai

Yayinda annobar korona ta yi karfi a kasar, kwamitin fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 1 ga watan Fabrairu, ta sanar da wasu jerin jihohi biyar da kananan hukumomi 22 a Najeriya da cutar COVID-19 ta yadu sosai.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Shugaban kwamitin PTF na kasa, Dr Sani Aliyu, ya gargadi yan Najeriya a kan zuwa wadannan jihohi da abun ya shafa, jaridar Punch ta ruwaito.

A cewarsa, wadannan jihohi da kananan hukumomi da abun yayi kamari ya haifar da kaso 95 bisa dari na yawan wadanda ke kamuwa da cutar a kullun.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: FG ta ƙara wa'adin haɗa lambar NIN da layin waya zuwa 6 ga watan Afrilu 2021

Ku hankalta! Wadannan ne jihohi 5 da kananan hukumomi 22 da FG ta ce cutar korona ta yadu sosai
Ku hankalta! Wadannan ne jihohi 5 da kananan hukumomi 22 da FG ta ce cutar korona ta yadu sosai Hoto: PTF on COVID-19
Source: UGC

Kamar yadda Legit.ng ta gano, ya bayyana jihohin a matsayin:

1. Yobe

2. Jigawa

3. Zamfara

4. Kebbi

5. Kogi

Aliyu ya bayar da sunayen kananan hukumomin da ke da matukar hatsari a matsayin:

Nkanu-West (Enugu)

Abuja Municipal Area Council (FCT)

Gwagwalada (FCT)

Gombe (Gombe state)

Chikun (Kaduna-North)

Kaduna South (Kaduna)

Nassarawa (Jihar Nasarawa)

Kano (Jihar Kano)

Katsina (Jihar Katsina)

Ilorin-South (Ilorin-West)

Eti-Osa (Ikeja, Lagos)

Kosofe (Lagos Mainland)

Keffi Lafia (Nasarawa)

Ibadan-North (Oyo)

Jos-North (plateau)

Jos-South (Plateau)

Port-Harcourt (Rivers)

Wamako (Sokoto).

Aliyu ya ce:

“Wadannan kananan hukumomi wadanda mafi akasarinsu a cikin birane ko manyan biranen jiha ne su haddasa sama da kaso 95 cikin 100 na annobar, musamman sabbin wadanda suka kamu a kasar.

“Bugu da kari, muna da jihohin da babu bayanansu. Idan baka yi gwaji ba, ba za a iya tantance bayananka ba. Idan ba a tantance bayananka ba, ba za mu san matakin da annobar ta kai ba a jiharka."

KU KARANTA KUMA: A yau Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Shugabannin SSANU da NASU

A wani labarin, mun ji cewa mutane 405 cutar Korona ta hallaka a watanni biyu da suka gabata, kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da cutar Coronavirus ta bayyana ranar Litinin.

Hakazalika ma'aikatan kiwon lafiya 75 suka kamu da cutar makon da ya gabata, hukumar hana yaduwar cututtukan a Najeriya (NCDC) ta bayyana.

Gwamnatin tarayya ta ce an gano sabon nauyin cutar COVID-19 da ta bulla a Birtaniya har guda bakwai a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel