Da ɗuminsa: FG ta ƙara wa'adin haɗa lambar NIN da layin waya zuwa 6 ga watan Afrilu 2021
- Yan Najeriya da dama na iya samun sassauci a zuciya yanzu kan lamarin da ya shafi hade layin wayarsu da NIN
- Hakan zai kasance ne sakamakon sabon umurnin da ke ƙara wa'adin haɗa lambar NIN da layin waya har zuwa tsawon makonni takwas masu zuwa nan gaba
- Ku tuna cewa shirin ya hadu da tangarda daban-daban irin su cunkoson jama’a da dai sauransu
Gwamnatin tarayya ta daga wa yan Najeriya da dama kafa kan shirin haɗa lambar NIN da layin waya wanda ke gudana a kasar.
Duba ga matsalolin da ake ta fuskanta, gwamnati ta kara wa'adin shirin har zuwa makonni takwas masu zuwa nan gaba.
KU KARANTA KUMA: A yau Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Shugabannin SSANU da NASU
Jaridar Punch ta ruwaito cewa daraktan harkokin labarai na hukumar sadarwa ta Najeriya, Ikechukwu Adinde ne yayi sanarwar.
Adinde ya ce ministan sadarwa, Isa Pantami ya isar da sakon a lokacin wata ganawa da kwamitin ministan kan rijistan NIN da Sim wanda ya gudana a ranar 1 ga watan Fabrairu, 2021.
Da wannan, sabon wa'adin rufe layukan a yanzu shine ranar 6 ga watan Afrilu 2021.
KU KARANTA KUMA: "Ba Arewa ba, sauran bangarori ne za su sha wahala idan da za a raba Najeriya"
A gefe guda, Kungiyoyin musulmi sun yi korafi kan yadda ake hana mata musulmi yin rajistan katin dan kasa saboda sun saka hijabi.
Hadakar kungiyoyin sunyi wannan koken na wurin taron ranar Hijabi na duniya (1 ga watan Fabrairu) inda suka yi kira ga hukumomi a Nigeria su dauki matakin hana wannan.
Kungiyoyin sun jadadda cewa kundin tsarin mulkin Nigeria ya bawa mata musulmi damar saka hijabi kuma ba dole sai sun cire za a iya daukan hotonsu ba idan dai fuska zai fito.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng