Wasu 'yan bindiga sun kai hari Giwa jim kadan bayan harin sojoji akan abokansu
- Wasu 'yan bindiga sun sake kai hari karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna, bayan sojoji sun gama kakkabe abokansu
- Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida a Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da sake kai harin 'yan bindigar a cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin
- A cewar Aruwan, 'yan bindigar sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane da dama
Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane da dama a kauyen Garawa, karamar hukumar Giwa jihar Kaduna.
Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan da rundunar sojin sama ta samu nasarar kakkabe wasu yan bindiga a garuruwan Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun.
Kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida, Mr Samuel Aruwan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kamar yadda The Nation ta rawaito.
Aruwan ya bayyana cewa hukumar tsaro na ci gaba da bincike kan harin da aka kai Giwa, yayin da aka tsaurara matakan tsaro a yankin.
Ya ce yan bindigar sun kai hari tare da kashe mutane biyu a wurare daban daban da ke a karamar hukumar.
KARANTA: Obasanjo: Akwai banbanci a tsakanin Buharin yanzu da wanda na sani a baya
A cewar sa, an kashe Alhaji Sa'adu a gundumar Fatika yayin da yan bindigar suka sace wasu mutane.
"Haka zalika, yan bindigar sun far wa kauyen Doka duk a cikin gundumar Fatika, inda suka yi garkuwa da wasu mutane.
KARANTA: Sabuwar cuta mai kumbura kafafu ta bulla a jihar Bauchi, ta kwantar da mutane goma
"A kauyen Angwan Dan Yaya, a wannan gundumar, yan bindigar sun kashe wani mutum mai suna Alhaji Suleiman Audu."
A baya Legit.ng ta rawaito cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya soki shugaba Muhammadu Buhari akan harkar tsaron ƙasar nan.
Mr Obasanjo, ya ce, abin takaici ne yadda shugaban kasa mai matsayin babban hafsan hafsoshin kasar nan ya gaza kawo karshen yan tayar da ƙayar baya.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi wannan furuci ne jiya Lahadi da masanin tarihin nan, Toyin Falola, inda ya buƙaci shugaban ƙasa mai ci da ya farka daga dogon baccin da yake yi.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng