Ku sabunta rajistarku da APC don ci gaba da zama a mukamanku, in ji Lalong

Ku sabunta rajistarku da APC don ci gaba da zama a mukamanku, in ji Lalong

- Gwamnan jihar Filato ya tabbatarwa mambobin majalisarsa cewa su gaggauta inganta rajistarsu

- Gwamnan ya jaddada cewa, matukar suna son ci gaba da zama a mukamansu to dole su sake rajistar

- Sai dai ya bayyana cewa ba yana tursasawa bane, yana son sanin matsayinsu ne don ci gaba da tafiya dasu

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya bukaci mambobin majalisar zartarwa ta jihar da su yi rajistar membobin da ke gudana da kuma sake jaddada zamansu 'yan jam’iyyar APC, domin su tsira da mukamansu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Lalong ya yi kiran ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin wakilan jam’iyyar zuwa jihar don atisaye.

“Don Allah membobin zartarwa, ku yi iyakar kokarinku, ku koma ku sake jaddada zamanku mambobi na jam’iyyar," in ji shi.

“Wannan shi ne abin da nake tsammani daga kowane mai ruwa da tsaki, na riga na fada musu cewa babu wanda ke karkashin nadin da yake da lasisin cewa, a’a, ba zan yi rajista ba.

KU KARANTA: An harbe 'yan ta'adda biyu tare da kame daya a jihar Adamawa

Ku sabunta rajistarku da APC don ci gaba da zama a mukamanku, in ji Lalong
Ku sabunta rajistarku da APC don ci gaba da zama a mukamanku, in ji Lalong Hoto: News Verge
Asali: UGC

“Idan baku yi rijista ba a da, wannan shine lokacin da za ku sake inganta alƙawarin da kuka yi.

“Idan ba ku son sake rattaba hannu a kan nadinku, to kuna iya gaya mana kun kasance daga wancan bangaren," in ji shi.

Gwamnan ya yaba wa jajircewar Shugaba Muhammadu Buhari kan wannan aiki, yana mai cewa wannan karimcin zai karfafa jam’iyyar tare da tabbatar da adalci wajen bayar da lada ga biyayya ga jam’iyyar.

Ya ce rajistar a matakan unguwanni za ta bai wa wadanda ke matakin farko mallaka da kuma jin na kasancewarsu a jami'iyyar, ya kara da cewa hakan zai kara musu kwarin gwiwa wajen marawa ayyukan jam’iyyar baya.

Ya ce aikin a bude yake, yana mai bayar da tabbacin cewa ba wani tursasawa ko magudi don samun alkaluman jabu.

Tun da farko, shugaban tawagar, Musa Mahmud, ya ce sun je Filato ne don sa ido kan aikin da kuma tabbatar da cewa an bi dukkan ka'idojin aikin.

Mista Mahmud ya ba da tabbacin cewa atisayen zai yi nasara, yana mai cewa "Mai martaba zai yi alfahari a karshen sa."

KU KARANTA: 'Yan Najeriya ne masu cin hanci da rashawa ba Buhari ba, Garba Shehu

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya ce maimakon a auna shi kuma a yaba masa kan ayyukan da gwamnatin sa ke yi, manyan kasar nan sun gwammace su zage shi, ReubenAbati ya ruwaito.

Ya yi magana ne bayan cin abincin rana da gwamnonin APC bayan sake tabbatar da kasancewarsa dan jam’iyyar a mazabarsa da ke Daura, Jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.