Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya nada sabon Shehun Dikwa

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya nada sabon Shehun Dikwa

- Biyo bayan rasuwar Shehun Dikwa a makon da ya gabata, an nada sabon Shehun na Dikwa

- Gwamna Babagana Umaru Zulum ne ya nada sabon Shehun a wata sanarwa da aka fitar

- An nada Abba Umar Jato ne a matsayin sabon Shehun Dikwa a fadar jihar Borno

Gwamnatin jihar Borno ta nada Abba Umar Jato a matsayin Shehun Dikwa, Daily Trust ta ruwaito.

Abba Umar Jato ya gaji marigayi Shehu Mohammed Ibn Shehu Masta II El-Kanemi, wanda ya rasu a makon da ya gabata.

Nadin nasa a matsayin mai fada aji na farko da Gwamna Babagana Zulum ya yi ya fito ne a cikin wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar.

KU KARANTA: Shugaban makaranta da aka sace ya kubuta daga hannun yan bindiga

Gwamna jihar Borno Babagana Zulum ya nada sabon Shehun Dikwa
Gwamna jihar Borno Babagana Zulum ya nada sabon Shehun Dikwa Hoto: News Reservoir
Asali: UGC

Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Usman Jidda Shuwa ne ya sanar da rasuwar Marigayi Shehu a garin Biu, jim kadan bayan gabatar da 'Staff of Office' ga Sarkin Biu, Alhaji Mai Mustapha Umar Mustapha da Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi a ranar Asabar da ta gabata.

An dauke shi zuwa Abuja kwana daya kafin rasuwarsa a ranar Juma’ar da ta gabata.

Wannan shi ne karo na uku a jerin wadanda suka mutu a jihar cikin kankanin lokaci, bayan na Shehun Bama da na Sarkin Biu a shekarar 2020.

KU KARANTA: EFCC ta damke wasu daliban makarantar damfara a Abuja

A wani labarin daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Talata ya ba da umarnin daukar likitoci 40 a matsayin kari kan yardarsa da ya yi a baya, domin biyan bukatun kula da lafiya na karuwar al’ummar jihar, Vanguard News ta ruwaito.

Shawarwarin na ranar Talata na zuwa ne watanni hudu bayan da Gwamnan ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 594.

Daga cikin wadanda za a dauka sun hada da: likitoci lafiya 86, ma’aikatan jinya 365 da ungozomomi, masu harhada magunguna 45 da kwararrun masana kiwon lafiya 100 da sauran ma’aikatan tallafi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.