Wata matashiya ta haifi tagwaye masu mabanbancin launin fata

Wata matashiya ta haifi tagwaye masu mabanbancin launin fata

- Wata matashiya mai suna Kayleigh Okotie ta haifi yaranta biyu, ta rungume su har tayi bacci

- Sai dai a lokacin da ta farka daga bacci, ta lura akwai wani abu na musamman game da su yaran

- Yaronta da yarinyarta suna da gashi daban-daban da kuma bambancin launukan fata

Mahaifiyar wasu yara tagwaye a kasar London Kayleigh Okotie tana rayuwa cikin mafarki.

Matashiyar mai shekaru 32 tana matukar alfahari da yadda tagwayenta suke da kyau da kuma yadda babu kama tsakanin jariran biyu.

Mahaifiyar da abokin tarayyarta Jordan King sun yi maraba da yaransu kuma sun lura cewa jariran suna da kamanni na musamman waɗanda ba kasafai suke faruwa a cikin yawancin tagwaye ba.

Na farko, suna da launuka daban-daban. Dayansu na da launi mai haske yayin da ɗayan ya kasance mai duhu, launin cakuleti.

KU KARANTA: Nigeria Main Labarai LABARAI An harbe 'yan ta'adda biyu tare da kame daya a jihar Adamawa

Wata matashiya ta haifi tagwaye masu mabanbancin launin fata
Wata matashiya ta haifi tagwaye masu mabanbancin launin fata Hoto:@turkiyegazetesi
Source: Twitter

Masana kimiyya suna kiran abin da ya faru a matsayin "genetic quirk."

Gashin Jaziyah mikakke ne yayin da na Naylah yana da duhu kuma murdadde.

Kayleigh ta gaya wa jaridar The Sun:

"Suna da kamanni daban-daban, abin birgewa ne a gani."

Mahaifiyar 'yan biyun ta nace cewa duk da cewa an haifi yaron da yarinyar a rana ɗaya, kamanninsu kamar na dare ne da rana.

Matashiyar mai shekaru 32 'yar asalin Turai da Najeriya ce amma har yanzu tana mamaki lokacin da ta ga jariran nata a karon farko.

Ta jima tana zazzafan nakuda, ta bayyana abinda ta iya yi bayan ta haifi yaran shine rungume yaran da yin bacci.

Lokacin da ta farka, Kayleigh ta lura cewa ta rasa cikakken bayani game da jariran nata.

KU KARANTA: Wata 1 da aurensa, 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe matashin jami'in Soja

Awani labarin, Kafin haihuwar 'yan hudun a ranar Juma'a, 5 ga watan Yuni, Hauwa'u ta haifi yara 13 a baya.

Yayin hirarta da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Talata, Hauwa'u ta ce yanzu tana da 'ya'ya 17 daga haihuwa takwas da ta taba yi.

An mayar da Hauwa'u da jariranta zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zaria domin samun kyakyawar kulawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel