Hotunan saukar Sunday Igboho jihar Ogun domin fatattakar Fulani makiyaya
- Wani matashi mai rajin kare hakkin yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya isa jihar Ogun
- Ya isa jihar ne da zafinsa don ya fatattaki kaf makiyayan da suke jihar kamar yadda yayi a jihar Oyo inda aka yi kaca-kaca da gidan Sarkin Fulani
- Ya ce wajibi ne su yaki Fulani don kawo karshen ta'addanci da cutarwar da suke yi wa 'yan uwansa yarabawa, kuma yana da magoya baya
Wani mai yakin kwatar 'yancin Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya isa jihar Ogun yana cewa ya kai ziyarar ne don ya fatattaki makiyaya.
Dama Igboho ya bayyana a labarai yana bai wa makiyayan da suke wuraren Ibarapa dake jihar Oyo wa'adin kwanakin da za su kwashe ya nasu ya nasu su bar garin. Bayan nan ne aka kai wa gidan sarkin fulanin yankin farmaki.
An samu labarin yadda aka lalata gidan har ana kona motocin da suke harabar gidan. Igboho ya bayyana wa manema labarai dalilin zuwansa garin.
KU KARANTA: Barawo ya sace sadaki N100,000 daga aljihun waliyyin amarya a masallacin Al Noor
Premium Times ta samu bidiyon tattaunawar da aka yi dashi inda yake cewa ya je ne don nema wa 'yan uwansa hakkinsu sakamakon yadda Fulani suke ta kashe su.
A cewarsa, wajibi ne Fulani su bar yankin yarabawa don a samu zaman lafiya da tsaro. Ya ce za su wuce Yewa ne don yakar Fulanin da suke addabar yarabawan jihar Ogun.
Ya kuma yaba wa yarabawan da suka mara masa baya da kuma gwamnan jihar Ogun bisa kaunar da yake nuna wa mutanensa.
KU KARANTA: Buhari ya tashi daga baccinsa, ya yaki 'yan bindiga dake 'bayan gidansa', Obasanjo
A wani labari na daban, sabbin hafsoshin tsaron kasar nan sun kai ziyararsu ta farko jihar Borno, jihar da ta kasance filin daga da 'yan Boko Haram.
Sun samu ganawa da Gwamna Zulum a Maiduguri, tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima ya samu halartar zaman.
Shugaban ma'aikatan tsaro, manjo Janar Leo Irabor ya jagoranci shugaban sojin tudu, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, shugaban sojin ruwa Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo da shugaban sojin sama, Air Vice Marshal isiaka Oladayo Amao zuwa gidan gwamnatin jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng