Ana handama, son kai da babakere wajen rabon N20,000 na Buhari, matan Kaduna

Ana handama, son kai da babakere wajen rabon N20,000 na Buhari, matan Kaduna

- A shirin gwamnatin Buhari na rabawa mata N20,000, akwai lauje cikin nada a rabon jihar Kaduna

- Wasu mata sun bayyana cewa ana sama-da-fadi da kudaden da ya kamata a basu a wajen rabon

- Rahoto ya bayyana cewa an ga wasu mata suna zuwa da motoci suna karbar kudin maimakon a bai wa talakawa

Wasu mata a jihar Kaduna sun koka kan zargin sama-da-fadi da son kai a cikin tallafin N20,000 da ke gudana wanda Ma’aikatar Kula da Jin Kai ta Tarayya ke yi a jihar, The Guardian ta ruwaito.

Matan sun yi magana da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Litinin a Kaduna a wurin da ake rabon kudin.

Ya ce mutanen da ba a san su ba suna karbar kudade daga wasu daga cikin wadanda suka amfana.

Sun yi zargin cewa akwai akasarin wadanda aka yi niyyar su ci gajiyar shirin kamar yadda aka tsara, inda suka kara da cewa wadanda suka amfana “galibi dangi ne da abokai na jami’ai da 'yan siyasa.’’

KU KARANTA: 'Yan Najeriya ne masu cin hanci da rashawa ba Buhari ba, Garba Shehu

Akwai sama-da-fadi, son kai da babakere wajen rabon N20,000 na Buhari
Akwai sama-da-fadi, son kai da babakere wajen rabon N20,000 na Buhari Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Daya daga cikin matan, Khadija Ahmad, ta shaida wa NAN cewa tallafin da aka tsara don bayar da hannun jari ga wasu ‘yan kasa masu fama da talauci da masu rauni suna karewa a aljihun wasu.

A cewar ta, wasu daga cikin matan da suka ci gajiyar sun tuko mota zuwa wurin a cikin motoci masu walƙiya da ke nuna alamar cewa ba sa buƙatar irin wannan tallafi.

Wata mata, Misis Rabi Mohammed ta ce an tattara sunayen kusan 50 daga cikinsu an ce su zo wurin taron a kungiyance, tana mai kuka cewa babu wani daga cikinsu da ya karbi kudin.

“Mun kasance muna zuwa nan kowace rana tsawon kwanaki uku da suka gabata, tare da wasun mu suna zuwa da misalin karfe 6:00 na safe amma basu sami komai ba.

Ta kuma yi zargin cewa wasu mata sun tara kudin a madadin wasu sunayen mata a jerin, “saboda kawai sun san wani a cikin tsarin, kuma ba mu yi hakan ba.

"Mun kuma ga an ba mutane biyar N20,000 su raba, maimakon N20,000 kowane, yayin da wasu da aka taimaka suka raba tsakanin N15,000 zuwa N17,000 ga mutanen da suka taimaka musu."

KU KARANTA: An harbe 'yan ta'adda biyu tare da kame daya a jihar Adamawa

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta fara raba wa matan karkara kudi Naira dubu 20 a karkashin shirin bayar da tallafi ga matan karkara 4,000 a jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar gwamnatin tarayya, za a zabi matan 4,000 a fadin kananan hukumomi 23 na jihar.

An gabatar da shirin a cikin shekarar 2020 don ci gaba da aiwatar da tsarin zamantakewa a Gwamnatin Shugaba Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel