Zai yi wahala a kyale mulkin Najeriya ya fada hannun Bola Tinubu inji Rufai Hanga

Zai yi wahala a kyale mulkin Najeriya ya fada hannun Bola Tinubu inji Rufai Hanga

- Sanata Rufai Hanga ya ce mulkin Najeriya zai yi wa Bola Tinubu wahala

- Tsohon shugaban CPC ya bayyana cewa an kassara Bola Tinubu a APC

- A cewarsa, gwamnoni sun daidaita shi da aka sauke Adams Oshiomhole

Tsohon abokin tafiyar Muhammadu Buhari, kuma shugaban jam’iyyar CPC na farko, Rufai Hanga ya yi magana game da 2023 a wata hira da jaridar Leadership.

Sanata Rufai Hanga ya shaida wa ‘yan jarida cewa ya na da labarin cewa wasu kusoshin jam’iyyar APC za su taka Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.

Rufai Hanga ya ce a baya, Asiwaju Bola Tinubu ya na rike da kusan 80% na jam’iyyar APC, amma yanzu wasu gwamnonin jam’iyyar sun samu sun ruguza masa lissafi.

‘Dan siyasar ya ce gwamnonin da suka sa aka sauke Adams Oshiomhole, za su yi duk abin da za su iya domin ganin cewa sun karbi shugabancin kasar a zaben 2023.

KU KARANTA: An dakatar da ma'aikata saboda binciken Bola Tinubu, Atiku Abubakar

“Na ji daga majiya mai karfi da tabbaci cewa ba za su bar shi ya je kusa da fadar shugaban kasa ba, kuma abin da yake faruwa kwanan nan ya tabbatar mani da haka.”

Ya ce: “An yi masa kafa. Da farko Tinubu ya na da 80% na jam’iyyar APC a tafin hannunsa, amma domin a ga bayansa, an samu an ruguza shugabnnin APC, an nada wasu”

A cewar Sanata Hanga, an yi wannan ne duk domin a ga bayan Bola Tinubu a takarar 2023.

“Saboda ace shugabanci ba zai taba zuwa gare shi ba, za su yi kokarin ganin mulki ya tsaya ga junansu. Domin haka ni a na wa, an gama da Tinubu tuni.” Inji Hanga.

KU KARANTA: Buhari zai jaddada katin zama 'dan jam'iyyar APC

Zai yi wahala a kyale mulkin Najeriya ya fada hannun Bola Tinubu inji Rufai Hanga
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: www.guardian.ng/opinion/between-2023-presidency-and-bola-tinubu
Asali: UGC

‘Dan siyasar na Kano ya ce APC ta na rushe wa domin Tinubu ba zai hada-kai da masu burin mulki ya koma kudu ba, yayin da sauran ‘yan jam’iyya ba su tare da su duka.

Kwanakin baya kun ji cewa daya daga cikin manyan 'yan siyasar Arewa, Alhaji Sule Lamido ya hango rushewar jam’iyyar APC nan da zabe mai zuwa na 2023.

Tsohon Gwamnan na Jigawa ya bayyana cewa kafin shekara 3, PDP za ta dawo ta karbe mulki daga hannun jam'iyyar APC mai rike da shugabancin Najeriya.

Sule Lamido ya ce jam’iyyar APC za ta wargaje kafin 2023, saboda dama Buhari ne kadai ya rike ta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng