Sule Lamido: Jam’iyyar APC za ta wargaje a 2023, saboda Buhari ne ya rike ta
- Alhaji Sule Lamido ya ce APC ba za ta zarce 2023 ta na mulkin Najeriya ba
- Tsohon Gwamnan na Jigawa ya ce Buhari ne abin da ya rike jam’iyyar APC
- ‘Dan adawar ya ce da Buhari ya tafi, to babu abin da zai hana APC watsewa
Tsohon gwaman jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi hasashe cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta wargaje nan da shekarar 2023.
Jaridar Daily Trust ta rahoto tsohon gwamnan ya na wannan bayani a jihar Kano, a wajen ganawarsa da sababbin shugabannin PDP 27 na Jigawa.
Babban jagoran hamayyar a Najeriya ya ce jam’iyyar APC za ta watse a 2023 ne saboda a wancan lokaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya nan.
A cewar tsohon gwamnan na Jigawa, shugaban kasar ne ya ke jawo wa jam’iyyar farin-jini, wanda ba zai yi mata amfanin komai nan da lokacin ba.
KU KARANTA: 2023: Wallahi, Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ba - Sule Lamido
“Shi (Buhari) ne abin da ya dunkule APC, shi ne wanda ya jawo aka kafa jam’iyyar.” Inji Sule.
Ya ce: “Sun yi amfani da Buhari su kai inda suka kai, shi ma ya yi amfani da su ya zama shugaban Najeriya. Sun gogi junansu, kowa ya ci amfaninsa.”
Sule Lamido wanda ya dade ya na siyasa ya ce yanzu aikin APC ya kare, ta cin ma manufarta.
Alhaji Sule ya ce jam’iyyar PDP za ta kifar da APC, ta dawo kan mulki a 2023, ta kuma ceci Najeriya. Ya ce har gobe PDP ta na nan da karfinta a kasar.
KU KARANTA: Buhari ya sare kan alkawarin da ya yi na kawo karshen cin hanci
“Hadin APC ba gamon-jini ba ne, taron son-kai ne, wanda ya rataya tsakanin tafiyar Buhari da mutanen Tinubu.” Ya ce a 2023, abin da ya hada su, ya raba su.
Duk da adawarsa, kwanakin baya kun ji Alhaji Sule Lamido, ya na cewa bai dace a rika wasu kiraye-kirayen tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.
Tsohon gwamnan Jigawan ta tabbatar da cewa wannan kiran ba zai samu goyon bayan shi ba.
Sule ya jaddada cewa bai da wata matsala tsakaninsa da shugaban kasa, ya kara da cewa yana kalubalansa ne saboda siyasa da kuma rashin tsaron fadin gaskiya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng