Shugaban makaranta da aka sace ya kubuta daga hannun yan bindiga
- Hukumar 'yan sanda sun tabbatar da kubutar wani shugaban makarantar sakandare da aka sace
- Iyalan shugaban makarantar sun shaidawa 'yan sanda haka ne ta wayar raho
- 'Yan sanda na ci gaba da binciken yadda kubutarsa ta auku a halin yanzu
Iliyasu Suleiman mai shekaru 50 kuma shugaban makarantar sakandaren gwamnati ta kwana a Lere a karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi ya kubutu kwana takwas bayan wasu 'yan bindiga sun sace shi.
Wata majiya daga dangi ta shaida wa Daily Trust a ranar Lahadi cewa an saki Suleiman da safiyar ranar Asabar.
Idan dai ba a manta ba, an sace shugaban makarantar da kuma Zulkifiru Mohammed mai shekaru 25 a ranar Asabar din da ta gabata a kauyen Kardam da ke karamar hukumar Tafawa Balewa.
KU KARANTA: EFCC ta damke wasu daliban makarantar damfara a Abuja
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi yunkurin yin garkuwa da Audita Janar na jihar Bauchi wanda ya samu raunuka daga harbin bindiga, basu samu nasara ba suka sace wadancan mutane biyu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da sakin shugaban makarantar. PPRO, DSP Ahmed Wakili wanda ya bayyana hakan a wata hira ta wayar tarho ya ce an saki mutumin ne a ranar Asabar amma ya lura cewa babu cikakken bayani kan ko an biya fansa don a sako shi.
KU KARANTA: COVID-19: Jihohi 7 a arewacin Najeriya za su mori tallafin $900,000
A wani labarin, An ceto matasa Takum 24 daga cikin 25 da masu satar mutane suka sace a hanyar Wukari - Takum a jihar Taraba.
Daily Trust ta tattaro cewa rundunar hadin kai na sjoji da 'yan sanda daga Benue da Taraba sun samu nasarar kubutar da matasan ne a wani samame da suka kai a cikin dazuzzukan da ke jihohin Taraba da Benue awanni kadan da suka gabata.
Baba Muhammed dan uwan wasu daga cikin matasan da aka kubutar ya shaida wa Daily Trust a wata hira ta wayar tarho cewa an ceto 24 daga cikin 25 da aka sace a ranar Laraba da ta gabata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng