Wani dan majalisa ya harbe wanda ake zargin dan fashi da makami ne

Wani dan majalisa ya harbe wanda ake zargin dan fashi da makami ne

- Wani dan majalisar tarayya dan jihar Sokoto ya samu nasarar aika wani dan fashi lahira

- Dan majalisar ya harbe dan fashin yayain da suka shiga gidansa yin sata da 'yan uwansa

- Rundunar 'yan sanda ta jihar sun tabbatar da faruwar hakan, yayin da suka kai dauki gidan dan majalisan

Wani dan majalisar wakilai, Abdullahi Balarabe Salame, ya ba da labarin yadda aka yi fashi a gidansa da ke Sakkwato inda ya harbe daya daga cikin ’yan fashin da makamin.

PM News ta ruwaito cewa dan majalisar mai wakiltar mazabar Gwadabawa da Illela na tarayya ya nuna hotuna don tabbatar da harin da 'yan fashin suka kai.

“Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukaki.

"A yau da misalin karfe 3 na safe, wasu ‘yan fashi da makami sun kawo min hari a gidana da ke Sakkwato amma cikin ikon Allah, na sami damar harbi na kashe daya (dan fashin) na kuma raunata wasu. Ina godiya," in ji dan majalisar.

KU KARANTA: EFCC ta damke wasu daliban makarantar damfara a Abuja

Wani dan majalisa ya harbe wanda ake zargin dan fashi da makami ne
Wani dan majalisa ya harbe wanda ake zargin dan fashi da makami ne Hoto: Premium Times
Source: UGC

Daya daga cikin hotunan da Salame ya watsa ya nuna yadda aka fasa kofar gidansa. Wani kuma yana nuna hula 'faze cap' ta baci da jini, takobi da kulki.

Kakakin rundunar 'yan sanda a Sakkwato, Muhammad Sadiq ya tabbatar da rahoton, inda ya ce, "'Yan sanda sun yi hanzari don taimakawa wajen dakile harin".

“Rundunar‘ yan sanda ta jihar Sakkwato na sane da yunkurin afkuwar fashi da makami a yankin Bado Quarters da ke Sakkwato, lamarin da ya gamu da cikas sakamakon hanzarin mayar da martani na hadin gwiwar ’yan sanda masu sintirin birane,” in ji shi a cikin wata sanarwa.

KU KARANTA: Mun cancanci girmamawa saboda aiki tukuru ba zagi ba, Inji Buhari

A wani labarin, An ceto matasa Takum 24 daga cikin 25 da masu satar mutane suka sace a hanyar Wukari - Takum a jihar Taraba.

Daily Trust ta tattaro cewa rundunar hadin kai na sjoji da 'yan sanda daga Benue da Taraba sun samu nasarar kubutar da matasan ne a wani samame da suka kai a cikin dazuzzukan da ke jihohin Taraba da Benue awanni kadan da suka gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel