Mun cancanci girmamawa saboda aiki tukuru ba zagi ba, Inji Buhari

Mun cancanci girmamawa saboda aiki tukuru ba zagi ba, Inji Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya koka kan yadda manyan Najeriya ke sukar gwamnatinsa

- Shugaban yace ya cancanci yabo ba suka ba idan aka yi duba da yanayin da ya samu kasar

- Ya kuma yi bayanin yadda harkar danyen man fetur ta tabarbare da ya gaji mulki a 2015

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya ce maimakon a auna shi kuma a yaba masa kan ayyukan da gwamnatin sa ke yi, manyan kasar nan sun gwammace su zage shi, ReubenAbati ya ruwaito.

Ya yi magana ne bayan cin abincin rana da gwamnonin APC bayan sake tabbatar da kasancewarsa dan jam’iyyar a mazabarsa da ke Daura, Jihar Katsina

Shugaban ya kafa hujja da furucin nasa ne a kan abin da ya ce shi ne yanayin rashin kyakkyawan abin da gwamnatinsa ta gada da kuma cewa dole ne ta aiki da karancin kayan aiki.

Ya sake nanata matsayinsa duk da irin makudan kudaden da gwamnatocin da suka gabata suke samu daga cinikin danyen mai, sun bar kadan don nunawa.

KU KARANTA: EFCC ta damke wasu daliban makarantar damfara a Abuja

Mun cancanci girmamawa saboda aiki tukuru ba zagi ba, Inji Buhari
Mun cancanci girmamawa saboda aiki tukuru ba zagi ba, Inji Buhari Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Don haka shugaban, ya bukaci mambobin jam’iyyar daga tushe su kare gwamnatinsa daga hare-haren wasu manyan kasar

Ya ce: "Matsalar ita ce zan so musamman manyan mutane su kasance masu tunani.

“Lokacin da muka zo, a ina muke, albarkatun da aka samu daga gare su da kuma yanayin abubuwan more rayuwa?

"Ya zama tilas in shawo kan lamarin, sau da yawa ina fadawa 'yan Najeriya cewa tsakanin 1999 zuwa 2014, su yi duba zuwa ga NNPC, su yi duba zuwa ga gwamnan Babban Bankin, ana samar da ganga miliyan 2.4 a kowace rana, matsakaicin kudin ya kasance $100 a kowace ganga."

Ya kuma koka kan yadda manyan kasar nan ke cin zarafin gwamnatinsa maimakon su yi duba da yanayin da ya tsinci kasar. Ya siffanta su da kau da ido ga alherin gwamnatinsa zuwa suka ga gwamnatin.

Yace "A'a, manyan'yan Najeriya ba su da sha'awar kimanta kokarinmu amma suna son sukar mu da duk kokarin da muke yi.

KU KARANTA: COVID-19: Jihohi 7 a arewacin Najeriya za su mori tallafin $900,000

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin ganawa da shugabannin hafsoshin kasar a ranar Talata ya ce gwamnatinsa ba ta samu sauki ba wajen cika alkawuran da ta dauka a shekarar 2015, Sahara Reporters ta ruwaito.

A cewar wata sanarwa da Adesina ya fitar, shugaban ya bukaci shugabannin hafsoshin da su kasance masu kishin kasa, yana mai cewa kasar na cikin yanayin neman taimakon gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel