Rashin tsaro: Masu satar Bayin Allah sun yi garkuwa da mutum 70 a Najeriya
- An kai hare-hare a jihohin Neja, Katsina, Kaduna, Taraba, da Delta a jiya
- ‘Yan bindiga sun yi gaba da mutane 75 a sanadiyyar wadannan hare-hare
- Bayan haka, rahotanni su na nuna cewa an hallaka mutane har kusan 20
Miyagun ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane su na cigaba da kai munanan hare-hare a Najeriya, su na satar Bayin Allah, har ma a kashe wasu.
Jaridar Punch ta fitar da dogon rahoto da ke nuna yadda ‘yan bindiga su ka sace mutane 75 da ake zargin za a yi garkuwa da su, sannan sun kashe mutum 18.
A jihar Neja, an yi awon-gaba da mutane akalla 50 a safiyar ranar Alhamis. Wannan abu maras dadi ya auku ne a yankin Bassa, a karamar hukumar Shiroro.
Har ila yau, ‘yan bindiga sun kashe mutane tara a kauyen Sarkin Sheme da ke garin Faskari, a jihar Katsina. Shi ma wannan ya faru ne duk a ranar Alhamis.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun mika wuya a Zamfara
A jihar Taraba kuwa, matasa 25 aka yi gaba da su yayin da su ke dawo wa daga bikin daurin aure a kan hanyar Wukari zuwa Takum, har yanzu babu labarinsu.
A daidai wannan lokaci ne kuma labari ya zo cewa ‘yan bindiga sun auka wa wasu kananan hukumomi uku a jihar Kaduna, inda su ka hallaka mutane hudu.
Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar cewa an kai hari a Igabi, Chikun da, Kujuru. A wajen harin ne aka rasa mutane biyu ‘yan bida daya.
Idan aka koma kudancin Najeriya kuwa, za a ji cewa miyagu sun kashe mutum akalla biyar a Warri.
KU KARANTA: Miyagu sun tare hanya, sun sace abokan ango a Wukari
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin hafsohin tsaro, wannan shi ne karo na biyu tun da ya hau mulki.
A karshen makon nan kuma kun ji yadda rikici tsakanin wasu kungiyoyin 'yan bindiga biyu ya kawo salwantar rayukan 'yan ta'adda masu yawa a jihar Katsina.
Wani dan bindiga ne ya sace matar takwarorinsa, kuma ya karbi N500,000 kafin ya fito da ita.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan rikicin ya barke ne tsakanin sansanin Mani Sarki da Dankarami da ke sansaniin Abu Rada a ranar Alhamis da ta gabata.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng