Sojin sama sun yi wa 'yan bindiga raga-raga a jihar Kaduna

Sojin sama sun yi wa 'yan bindiga raga-raga a jihar Kaduna

- Sojin saman Najeriya sun yi wa 'yan bindiga ruwan wuta a wasu kananan hukumomin Kaduna

- Sun halaka 'yan bindiga masu tarin yawa a Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun duk a ranar Alhamis

- Ta jiragen yaki dakarun sojin suka dinga hango 'yan bindiga suna al'amuransu dauke da shanu

Dakarun sojin saman Najeriya a ranar Alhamis sun kashe 'yan bindiga masu yawa a samamen da suka kai ta jiragen yaki a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun.

Kwamishinan tsaro na cikin gida, Samuel Aruwan, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis, Premium Times ta wallafa.

Ya ce yankunan da aka yi wannan aikin sun hada da babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari, Buruku, Ungwar Yako, Udawa, Polewire, Crossing Point, Gagafada, Kugu, Kamfani Doka, Gwaska, Goron Dutse da yankunan masu kusanci da nan.

"An hango 'yan bindiga tare da shanu a nisan kilomita 9 na arewacin Gidan Audu kuma duk an halaka su. Hakan ce ta faru a kudu maso yamma na yankin.

KU KARANTA: Mutum 2 sun sheka lahira yayin da bata-gari suka yi yunkurin balle ofishin 'yan sanda

Sojin sama sun yi wa 'yan bindiga raga-raga a jihar Kaduna
Sojin sama sun yi wa 'yan bindiga raga-raga a jihar Kaduna. Hoto daga @Premiumtimes
Source: Twitter

“An ga wasu 'yan bindigan a Gbakopai kuma an murkushesu. A kusa da wani tsauni da ke kauyen yammaci, an ga wasu 'yan bindigan da shanu kuma ba a sassauta musu ba.

“Hakazalika, dauke da makamai aka hango wasu 'yan bindigan a Gagafada yayin da suke kokari tsallakawa zuwa Polewire zuwa Kampanin Doka amma mayakan jiragen yakin suka halaka su.

“A yankin Gadani, an ga tawagar 'yan bindigan a babura 12 suna tsallaka dogo kuma an halaka su.

“Wasu 'yan bindiga a kan babura da ke tsallakawa daga kauyen Kwafe ba a barsu da ransu ba domin kuwa sun sha ruwan alburusai."

Kwamishinan ya ce dakarun sojin saman sun yi makamancin wannan aiki a karamar hukumar Giwa.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Ka bai wa sabbin hafsoshin tsaro wa'adin kawo canji, Ndume

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da hadimin wani dan majalisa mai wakiltar Oru ta yamma dake jihar Imo, Dominic Ezerioha.

Sun yi garkuwa da Chetachi Linus Igboenyesi, wanda aka fi sani da London Biggy da misalin karfe 11:34pm na ranar Talata, 26 ga watan Janairu yayin da yake hanyar zuwa garin Uli na jihar Anambra.

A wani bidiyo da wasu ganau suka dauka, anga inda 'yan bindigan suka ragargaza tagar motar wanda suka yi garkuwa dashi kafin su sace shi su yi awon gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel