'Yan bindiga sun halaka mutum hudu a Kaduna

'Yan bindiga sun halaka mutum hudu a Kaduna

- Yan bindiga sun kai hari a wasu garuruwa da jihar Kaduna sun halaka mutane hudu

- Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya nuna bakinsa kan afkuwar lamarin tare da yi wa iyalansu ta'azziya

- Gwamnan ya kuma umurci jami'an tsaro su gudanar da cikakken bincike a kan lamarin

A kalla mutane hudu ne suka rasa rayyukansu yayin wani hari da yan bindiga suka kai a garuruwa a kananan hukumomin Igabi da Kajuru a jihar Kaduna, The Channels ta ruwaito.

Yan bindigan a cewar kwamishinan tsaro da harkokin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, sun kai hari a garin Nasarawa Kalgo da ke kusa da Jaji, da Rigachikun a karamar hukumar Igabi inda suka kashe Harisu Ibrahim.

'Yan bindiga sun halaka mutum hudu a Kaduna
'Yan bindiga sun halaka mutum hudu a Kaduna. Hoto: @Channelstv
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga 7 sun ajiye makamai sun mika wuya da kansu a Zamfara (Hotuna)

Kazalika, yan bindiga sun kai hari a Kujama a karamar hukumar Chikun amma daga bisani yan banga sun fattake su.

Sai da a yayin da suke komawa mabuyarsu, yan bindigan sun kai hari a kauyen Janwuriya da ke karamar hukumar Kajuru inda suka kashe yan uwa biyu, Nuhu Ishaya da Yakubu Ishaya.

A wani harin na daban, yan bindigan sun kai hari a Maraban Kajuru, a karamar hukumar Kajuru inda suka kashe wani mazaunin garin, Samiru Na Yau.

KU KARANTA: Shekau ya fitar da sabon sautin murya, ya gargadi sabbin shugabanin sojoji da Buhari ya naɗa

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya nuna bakin cikinsa kan rasuwarsu ya yi addu'a Allah ya jikansu ya gafarta musu yayin da ya ke aike da sakon ta'aziyya ga iyalansu.

Gwamnan ya kuma bukaci jami'an tsaro su gudanar da bincike kan lamarin.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel