Dalilin da yasa ba zan goyi bayan tsige shugaban kasa Buhari ba, Lamido

Dalilin da yasa ba zan goyi bayan tsige shugaban kasa Buhari ba, Lamido

- Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan Jigawa ya ce bai dace a dinga kiraye-kirayen tsige Buhari ba

- Ya tabbatar da cewa wannan lamarin ba zai samu goyon bayan shi ba ko kadan

- Ya sanar da hakan ne a wani taron rantsar da shugabannin kananan hukumomi na Jigawa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce kiraye-kirayen da ake yi a kan tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga mulki bai dace ba kuma ba zai samu goyon bayansa ba.

Lamido, wanda ya sanar da hakan ga manema labarai yayin taron rantsar da shugabannin kananan hukumomi 27 da aka zaba a jiharsa, ya ce hakan kira ne kwatankwacin wanda ya dinga yi ga shugaban kasan.

Tsohon gwamnan wanda ya jaddada cewa bashi da wata matsala a tsakaninsa da shugaban kasa, ya kara da cewa yana kalubalansa ne saboda siyasa kuma da iya fadin gaskiyarsa.

Dalilin da yasa ba zan goyi bayan tsige shugaban kasa Buhari ba, Lamido
Dalilin da yasa ba zan goyi bayan tsige shugaban kasa Buhari ba, Lamido. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Ceton yaran Kankara: Wasu mutane suna cike da bakin ciki, Hadimin Buhari

Tsohon gwamnan, wanda ya yi magana a kan lamurran kasar nan daban-daban, ya tabbatar da cewa har yanzu lokacin cikar burinsa bai yi ba.

Ya kara da cewa abinda jam'iyyar PDP take bukata a halin yanzu shine daidaituwa da kuma hadin kai baki daya, jaridar Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Da duminsa: Hotunan 'yan makarantar Kankara suna isa gidan gwamnatin Katsina

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin tsaron kasar nan, inda yace abubuwa ba za su cigaba da faruwa haka ba a 2021.

Shugaban kasa ya sanar da hakan ne yayin bayyana farin cikinsa a kan sakin daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa ba zai ci amanarsu ba. Ya ce hankalinsa yayi matukar tashi a kan matsalar rashin tsaron da wasu bangarorin kasarnan suke ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel