2023: Wallahi, Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ba, Sule Lamido

2023: Wallahi, Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ba, Sule Lamido

- Alhaji Sule Lamido, ya yi sharhi a kan zaben 2023 da takarar APC

- Tsohon gwamnan na Jigawa ya rantse cewa Shugaban kasa Buhari ba zai taba marawa takarar Tinubu baya ba a 2023

- Lamido ya kuma kalubalanci mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da ya nuna mutanen da suka fitar daga kangin talauci a jihar Jigawa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba goyon bayan takarar shugabancin babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu ba.

An tattaro cewa mista Tinubu bai sanar da kudirinsa na takarar Shugaban kasa a 2023 ba a hukumance.

Sai dai kuma yayinda yake gabatar da jawabi a yayin rantsar da kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP a Dutse a ranar Laraba, Lamido ya ce Shugaban kasar ba zai cika alkawarin yarjejeniyar da suka kalla ta bangarensa ba, bayan ya samu goyon bayan shugabanni daga kudu maso yamma.

2023: Wallahi, Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ba, Sule Lamido
2023: Wallahi, Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ba, Sule Lamido Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Kwantan ɓauna: Yan bindiga sun kashe jami'an sa-kai 7 a Niger

A cewarsa, jam’iyyar mai mulki ta mutane biyu ne wato Buhari da Tinubu, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce: “Jam’iyyar APC mai mulki ta mutane biyu ce: Buhari da Tinubu kuma ina son fada maku cewa Wallahi! Wallahi! Buhari ba zai taba marawa Tinubu baya ba a zabe mai zuwa.”

A cewar tsohon ministar harkokin wajen, Buhari ya cika kudirinsa na mulkar kasar sau biyu a matsayin shugaban kasa ba tare da ya cimmaa manyan ajandarsa guda uku na magance rashin tsaro, cin hanci da rashawa da farfado da tattalin arziki.

Mista Lamido ya yiikirarin cewa Buhari ya yaudari yan Najeriya kamar yadda Donald Trump yayi wa kasar Amurka.

Ya yi zargin cewa mafi akasarin yan Najeriya sun daburce saboda tsarin shugabancin APC a kasar.

Ya kuma kalubalanci mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ya nuna wadanda aka fitar daga kangin talauci ta gwamnatin APC a jihar Jigawa.

KU KARANTA KUMA: A daina yi wa makiyaya kudin goro, suna da yancin zama a duk inda suke so, Shehu Sani ga Akeredolu

“Ina kalubalantar jawabin mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da ke cewa an fitar da yan Najeriya miliyan 20 daga kangin talauci. Muna so mu san wadanda aka fitar daga talauci a jihar Jigawa,” in ji Mista Lamido.

A wani labarin, Attahiru Dalhatu Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Sokoto, ya bayyana dalilin da yasa shugabannin arewa suka dawo daga rakiyar Buhari.

Kazalika, tsohon gwamnan ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari akan kashe makudan kudi domin sayen allurar rigakafin korona.

Bafarwa ya bayyana cewa matsalar Nigeria ta tsaro ce ba annobar cutar korona ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng