Da alamun za a je aikin Hajji bana

Da alamun za a je aikin Hajji bana

- Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta buɗe ƙasar rajistar aikin Hajjin 2021

- Hukumar ta bayyana sa ran ta cewa Saudiyya za ta iya ba da damar aikin Hajjin

- Hukumar ta umarci jihohi da su fara rajistar Hajjin da Umarah na 2021

Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), a ranar Litinin, ta fada wa shugabannin hukumomin mahajjata na jihohi su ci gaba da rajista da shirye-shiryen aikin Hajji da Umrah na 2021.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban ta na Hulda da Jama'a, Fatima Sanda, Shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunke Hassan, ya ce dage dakatarwar jiragen saman kasashen duniya da Masarautar Saudi Arabiya ta yi, ya ba da babban fatan yiwuwar maniyyatan su tashi domin aikin Hajji da Umrah a bana.

KU KARANTA: Da alamun an sace mai kamfanin Alibaba

Masarautar, a shekarar da ta gabata, ta dakatar da duk jirage na kasa da kasa da ke shigowa cikin kasar saboda annobar COVID-19, lamarin da ya haifar da mahajjata 1,000 ne kawai suka gudanar da aikin hajjin na shekarar 2020, wanda hakan ya rage yawan musulmai miliyan biyu da ke gudanar da aikin hajjin na shekara.

Da alamun za a je aikin Hajji bana
Da alamun za a je aikin Hajji bana Credit: Daily Trust
Asali: Facebook

Ya tabbatar wa Musulmin Najeriya cewa da zaran masarautar ta sanar da sabbin ka'idoji kan aikin Hajji da Umrah, hukumar za ta dauki matakan da suka dace don amfanin maniyyatan.

KU KARANTA: COVID-19: Tashin hankali a Poland

"A halin yanzu, hukumar ta bukaci maniyyata, jihohi da sauran masu aikin hajji da Umrah masu lasisi da su ci gaba da shirye-shirye da rajista yayin da suke yin hakuri har sai Saudiyya ta bayar da cikakkun bayanai."

A wani labarin daban, Saudiyya a ranar Lahadi ta sanar da sake bude kan iyakoki da kuma dawo da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa bayan dakatarwar da aka yi ta makwanni biyu da nufin dakile yaduwar wata sabuwar cutar ta Covid-19.

Gwamnatin ta ba da umarnin a dauke "matakan kariya da suka shafi yaduwar wani sabon nau'in kwayar cutar corona," in ji ma'aikatar cikin gidan, a cewar kamfanin dillancin labarai na Saudi Arabia.

Saudi Arabiya ta bayyana samun sama da mutane 363,000 da suka kamu da cutar, ciki har da sama da mutane 6,200 da suka mutu - mafi girma a tsakanin kasashen larabawan Tekun Fasha - amma kuma ta bayar da rahoton yawan samun sauki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.