NIMC ta bai wa MTN, Airtel, da sauran wasu kungiyoyi lasisin yin NIN

NIMC ta bai wa MTN, Airtel, da sauran wasu kungiyoyi lasisin yin NIN

- Ma'aikatar sadarwa ta bai wa kamfanonin sadarwa lasisin yiwa 'yan Najeriya rajistan NIN

- Ma'aikatar an bayyana ta duba ne da korafin ma'aiktan NIMC na yawan cincirindo da suke fuskanta a ofisoshinsu

- Sai dai har yanzu ma'aikatar ba ta kara wa'adin da a ka bayar na rufe rajistan ba

An bai wa kamfanonin sadarwa lasisin yin rajistar mutanen da ba su da Lambobin Shaidar zama dan Kasa don rage dumbin jama’a a ofisoshin Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa, in ji NIMC.

Darakta-Janar na NIMC, Aliyu Aziz, ya ce wasu sauran kungiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati su ma hukumar ta ba su lasisi don samar da NINs domin magance cincirindon jama’a a ofisoshin hukumar.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun mamaye sansanonin Boko Haram dake dajin Sambisa

NIMC ta bai wa MTN, Airtel, Da Sauransu lasisin yin NIN
NIMC ta bai wa MTN, Airtel, Da Sauransu lasisin yin NIN Hoto: Economic Confidential
Asali: UGC

Wannan ya zo ne yayin da ma’aikatan hukumar suka fada a ranar Talata cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Pantami, ya kafa kwamiti don magance bukatun ma’aikatan NIMC.

Da yake amsa tambayoyi game da matakan da NIMC ta dauka dangane da korafin da ‘yan kasa da kuma cincirindon jama’a a ofisoshin hukumar, Aziz ya ce an bai wa kamfanonin sadarwa na wayar salula ikon bayar da lambobin na ainihi.

"Mun ba da lasisi ga kungiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati da suka hada da telcos (kamfanonin sadarwa) don samar da wasu cibiyoyi," kamar yadda ya bayyana a cikin sakon WhatsApp ga wakilin PRNigeria.

KU KARANTA: Inganta asibitoci ya fi sayen rigakafin COVID-19, Bill Gates ga Buhari

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta ce lambar shaidar dan kasa ya zama tilas ga jami’an diflomasiyyar kasashen waje da za su ci gaba da zama a Najeriya na tsawon shekaru biyu ko sama da haka, jaridar Punch ta ruwaito.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Dr Isa Pantami, ne ya fadi hakan a cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Fasaha, Dr Femi Adeluyi, ya fitar a ranar Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.