Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya sallami Janar Buratai, da sauran hafsosin tsaro, ya nada sabbi

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya sallami Janar Buratai, da sauran hafsosin tsaro, ya nada sabbi

- Daga karshe, shugaba Buhari ya nada sabbin hafsoshin tsaron Najeriya

- Daga cikin wadanda aka nada akwai yan Arewa biyu da yan kudu biyu

- Wanda ya zama shugaban hafsoshin tsaron shine babba jarumin da ya yaki Boko Haram a baya

Bayan kiraye-kiraye daga yan majalisun tarayya da manyan masu ruwa da tsaki a Najeriya suka yiwa shugaba Buhari ya sallami hafsoshin tsaro kuma ya nada wasu, Buhari ya amsa a yau.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya a ranar Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, kuma ya nada sabbi ba tare da bata lokaci ba.

Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita.

A cewar Adesina, Buhari ya nada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin shugaban hafsoshin tsaro; Manjo Janar Ibrahim Attahiru matsayin shugaban Sojin kasa; RA AZ Gambo matsayin shugaban sojin ruwa, da kuma AVM IO Amao matsayin shugaban mayakan sama.

KU KARANTA: Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)

KU DUBA: An taba tsige Janar Attahiru Ibrahim a kan rikicin Boko Haram a shekarar 2017

A ranar Litinin, 25 ga watan Junairu, 2021, Alhaji Lai Mohammed, ya ce dakarun sojojin kasa sun hallaka ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda 158.

Ministan yada labarai da al’adun Najeriya ya ce dakarun sojojin sun yi wannan namijin kokari ne daga farkon shekarar nan ta 2021 zuwa yanzu.

A cewar Mai girma Ministan, sojojin sun samu wannan nasara ne bayan an fito da sababbin dabaru, jaridar The Nation ta fitar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel