Bayan wata da watanni, maganganun mutane sun sa an yi waje da Shugabannin Soji

Bayan wata da watanni, maganganun mutane sun sa an yi waje da Shugabannin Soji

- A karshe bayan tsawon shekaru kusan biyar da rabi, an yi sababbin Hafsohin tsaro

- Ta’adin ‘Yan bindiga da garkuwa da mutane su ka jawo nadin sababbin Hafsun Sojoji

- Mutane, kungiyoyi da manyan kasa sun dade su na kira a sauke shugabannin tsaron

Bayan tsawon watanni ‘yan majalisa, kungiyoyi masu zaman kansu, da shugabannin kabilu su na ta magana, shugaban kasa ya canza hafsun sojojin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto game da yadda yawan bakin mutane ya jawo shugaba Muhammadu Buhari ya nada sababbin shugabannin tsaro na kasa.

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa gazawar shugabannin tsaron na kawo karshen masifar garkuwa da mutane da ta’adin ‘yan bindiga, ya sa su ka rasa aikinsu.

Hafsun sojojin ba su iya kawo karshen matsalolin rashin tsaron da ake fama da su a Najeriya ba.

KU KARANTA: Hafsun Sojoji: Manyan Kudu sun zargi Buhari da rashin kaunar Ibo

Tun farkon shekarar nan hafsun sojojin suke tsammanin za a sallame su bayan alakarsu da mahukunta kasar ta fara canza wa, sai a makon nan aka yi waje da su.

A watan Disamban 2020, shugaba Muhammadu Buhari ya fara kyankyansa cewa zai yi canji. Ya ce: “Game da harkar tsaro, ina sa ran shekarar badi ta zama dabam.”

Da ya ke jawabi bayan an ceto ‘yan makaranta a Kankara, jihar Katsina, Buhari ya tabbatar da cewa a 2021 zai zama akwai aiki gaban hafsun sojojin da za su rage a ofis.

A bangaren tsofaffin hafsun sojojin, ba zai yiwu su yi murabus ba, domin ajiye aikin na su zai sa a zarge su da yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Bayan wata da watanni, maganganun mutane sun sa an yi waje da Shugabannin Soji
Tsohon shugaban Soji Janar TY Buratai Hoto: Twitter
Source: Twitter

KU KARANTA: Akwai sabani tsakanin T.Y Buratai da sabon COAS, Janar Ibrahim Attahiru

Ana sa ran sabon hafsun, Janar Leo Irabor ya jagoranci harkar tsaro ta yadda za a samu zaman lafiya. Ana zargin wanda ya rike kujerar kafinsa, bai yi abin da ya dace ba.

Bayan nadin hafsun sojojin da aka yi a ranar Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, mun ji cewa akwai yiwuwar wasu manyan sojojin kasa su bada wuri, su tafi ritaya.

Gidan Soja zai yi aman Janarori kimanin 20 ne domin a ba wasu manyan Sojoji dama su tashi

Wata majiya ta shaida wa 'yan jarida cewa wannan nadi da ka yi ya sa ‘yan ajin kwas 34 da 35 za su yi ritaya tun da an ba takwarorinsa shugabancin gidan sojan Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel