Shugaban Najeriya ya fadawa Hafsun Soji, su nuna kishi, su yi wa kasa aiki da kyau
- A yau ne shugaban kasa ya yi zama da sababbin shugabannin sojoji a Aso Villa
- Wannan ne karon farko da Muhammadu Buhari ya hadu da sababbin hafsoshin
- Buhari ya yi kira ga hafsoshin tsaron su yi kokari, su kawo zaman lafiya a kasa
A ranar Laraba, 27 ga watan Junairu, 2021, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi zaman farko da sababbin shugabannin hafsun sojojin Najeriya.
Shugaban Najeriyar ya yi kira ga sababbin hafsun tsaron bukatar su nuna kishin kasa, su yi aiki da kyau.
Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar da jawabi bayan zaman dazu.
Kamar yadda Garba Shehu ya bayyana, Ministan tsaro na kasa, Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ne ya jagoranci hafsun sojojin zuwa wajen shugaban kasa.
KU KARANTA: Abubuwan da su ka ci kujerar Buratai, Siddique, dsr
“Muna cikin wani mawuyacin yanayi. Ku nuna kishin kasa, ku yi wa kasa aiki, ita ku ke yi wa bauta.”
“Babu abin da zan iya fada maku domin a cikin wannan aiki ku ke. Ni ma ina ciki a da, kuma zan yi maku addu’a.” inji shugaban kasar.
“Ina so kuma in tabbatar maku da cewa zan yi duk abin da zan iya a matsayina, saboda mutane su yaba da kokarinku."
"Kun san halin da mu ke ciki a 2015, kun san yadda mu ke a yau, da irin nasarorin da mu ka samu. Buhari ya ce ya yi alkawarin zai samar da tsaro a Najeriya."
KU KARANTA: Buhari da Hafsun Sojoji sun hadu
A cikin alkawuran da shugaban kasar ya yi na kawo zaman lafiya, yaki da rashin gaskiya da farfado da tattalin arziki, ya ce aikin akwai wahala, amma ana nasara.
Janar Leo Irabor ya yi jawabi bayan taron a madadin sauran abokan aikinsa, ya ce Buhari ya fada masu cewa ana da sa ran za su yi kokari, don haka sai sun dage.
Wasu sun fara kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari ya binciki Janar Buratai da sauran Hafsun Sojoji.
Jam'iyyar PDP ta ce binciken Hafsun Sojoji da aka cire zai taimaka wajen kawo zaman lafiya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng