Rahoto: Za a yi wa Jami’an Sojoji akalla 20 ritaya saboda nadin shugabannin hafsun Sojoji

Rahoto: Za a yi wa Jami’an Sojoji akalla 20 ritaya saboda nadin shugabannin hafsun Sojoji

- Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sababbin Hafsun Sojoji a Najeriya

- Za a iya yi wa wasu manyan Jami’ai ritaya tare da tsofaffin hafsun Sojojin

- An sallami ‘yan kwas na 33, saura ‘yan aji na 34 da 35 ne suka rage a gidan

Watakila jami'an sojoji da-dama ‘yan ajin kwas na 34 da 35 za a yi wa ritaya a sakamakon nadin sababbin hafsun sojoji da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Wata majiya ta shaida wa jaridar Punch cewa wannan nadi da ka yi ya sa ‘yan ajin kwas 34 da 35 za su yi ritaya tun da an ba takwarorinsa shugabancin gidan soja.

Manjo Janar Lucky Irabor da zai rike shugaban hafsun tsaro ya na cikin ajin kwas na 34, shi kuma Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya na sahun ‘yan kwas na 35.

Wani babban jami’in da ake tunanin za ayi wa ritaya kwanan nan shi ne Laftana-Janar Lamidi Adeosun, wanda aka kara wa matsayi har ya kamo T. Y Buratai.

KU KARANTA: Babu Inyamuri ko daya a cikin sababbin Hafsun Sojojin da aka nada

An yi ta tunanin shugaban kasa zai ba Lamidi Adeosun wanda ke kula da horas wa da aikin sojojin wata kujera, ganin karin girman da aka yi masa a 2019.

Jaridar ta ce a al’ada wadanda ke gaban hafsun sojojin da wasu manyan jami’ai za su basu wuri, wannan ya sa wasu Janar na sojojin kasar za su fuskanci ritaya.

Majiyar ta ce amma akwai yiwuwar a rike wasu daga cikin jami’an da za su taimaka wa sababbin shugabannin tsaron wajen yakin da ake yi da 'Yan Boko Haram.

Haka zalika kuma za a iya kai wasu sojojin zuwa hedikwatar tsaro na kasa baki daya, inda za su yi aiki ba tare da sun zauna karkashin Janar Ibrahim Attahiru ba.

KU KARANTA: Buhari ya sallami Buratai, ya nada sababbin Hafsun Sojoji

Rahoto: Za a yi wa Jami’an Sojoji akalla 20 ritaya saboda nadin shugabannin hafsun Sojoji
Sababbin shugabannin hafsun Sojoji Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoton ya kuma tabbatar mana akwai sabani tsakanin T.Y Buratai da magajinsa, Ibrahim Attahiru.

A ranar Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, shugaba Muhammadu Buhari ta bakin hadiminsa, Femi Adesina, ya bada sanarwar canza shugabannin hafsun tsaro.

Sababbin sojojin da za su rike shugabanci sune: Manjo Janar Lucky Irabor; Manjo Janar I. Attahiru; Rear Admiral A.Z Gambo, da Air-Vice Marshal I. Amao.

Idan za ku tuna wadanda aka yi wa ritaya su ne Janar Abayomi Olonisakin; Laftana Janar Tukur Buratai; Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas da Air Marshal Sadique Abubakar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng