An taba tsige Janar Attahiru Ibrahim a kan rikicin Boko Haram a shekarar 2017
- A 2017 aka nada Attahiru Ibrahim ya jagoranci Operation Lafiya Dole
- Amma kafin a je ko ina, Janar Tukur Buratai ya tsige Attahiru Ibrahim
- Ba a bada dalilin tsige shi ba, amma Boko Haram sunyi ta’adi a lokacin
A ranar 26 ga watan Junairu, 2021, aka bada sanarwar cewa Manjo-Janar Attahiru Ibrahim, ya zama sabon shugaban hafsun sojojin kasan Najeriya.
Kusan shekaru uku da su ka wuce kenan da shugaban hafsun sojojin kasa mai barin-gado, Lafatana-Janar Tukur Yusuf Buratai ya tsige Janar Attahiru Ibrahim.
Shugaban sojojin kasa na wancan lokaci ya sauke Attahiru Ibrahim ne a sakamakon yin kasa a gwiwa a yakin da ake yi da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram.
Jaridar The Cable za a iya tuna cewa a watan Yulin 2017, Tukur Buratai ya ba Attahiru Ibrahim wa’adin kwanaki 40 ya kawo masa kan Abubakar Shekau.
KU KARANTA: Buhari ya sallami Buratai, ya nada sababbin Hafsun Sojoji
Janar Attahiru Ibrahim bai yi nasarar hakan ba, har gobe kuma shugaban ‘yan ta’addan bai shiga hannu ba.
A karshe sai aka ga hare-haren mayakan ta’adda ya karu, aka rika kai wa jami’an tsaro farmaki har gidan soja, a wannan lokaci ne kuma harin bakin wake ya yawaita.
Asali ma abin da ya faru shi ne, bayan wata daya da nada Ibrahim a matsayin shugaban sojojin da ke yaki da Boko Haram, ‘yan ta’addan suka kai hari har Maiduguri.
A wannan lokaci ne kuma sojojin kungiyar Boko Haram suka kai wa wasu masana daga jami’ar Maiduguri farmakin da su ka yi nasarar kashe wasu sojojin kasa 12.
KU KARANTA: An ba Shugaban Operation Lafiya Dole wa'adin cafko Shekau
‘Yan ta’addan sun kuma yi nasarar hallaka wasu ma’aikatan NNPC a wannan harin da su ka kai. Daga baya an kai hari a wani masallaci inda aka kashe mutane 50.
Watanni shida da nada wannan jami’i, Janar Tukur Buratai ya fahimci gazawarsa, ya fatattake shi daga ofis, ya nada Manjo-Janar Rogers Nicholas a madadinsa.
A ranar 6 ga watan Disamban 2017, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya tsige babban kwamandan Sojoji a filin daga dake jihar Borno.
A wata sanarwa da ta fito daga Janar Sani Usman Kukasheka, Manjo Janar Nicholas ne ya maye gurbin Attahiru Ibrahim a matsayin jagoran Operation Lafiya Dole.
A wannan lokaci mayakan kungiyar Boko Haram sun yi ta kai munanan hare-hare a yankin arewa maso gabas, musamman a jihohin Adamawa, Yobe, da Borno.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng