Takaiccen labarin Manjo Janar Adeosun da ya zama Laftana Janar a farat daya

Takaiccen labarin Manjo Janar Adeosun da ya zama Laftana Janar a farat daya

A jiya Talata 9 ga Watan Yulin 2019, a ka samu labarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhai ya hanzarta ya karawa Manjo Janar Lamidi Adeosun matsayi a gidan soja zuwa mukamin Laftanan Janar.

Mun kawo maku kadan daga cikin tarihin wannan babban Soja kamar yadda Jaridar nan ta Daily Trust ta tsakuro:

1. An haifi Lamidi Adeosun ne a Garin Ola Oluwa a cikin jihar Osun a Agustan shekarar 1963.

2. Lamidi Adeosun ya shiga gidan Sojan Najeriya ne yana da kusan shekaru 20 a Duniya a 1983.

3. Adeosun ya kammala karatu da horan Soja har ya zama ya kai Manjo Janar a tsakiyar 2014.

4. Babban Sojan kasar ya yi aiki a matsayin babban kwamanda watau GOC na Lardin Maiduguri.

5. Janar Adeosun ya koma Hedikwata a 2017 inda ya jagoranci harkar horas da Sojojin Kasar.

KU KARANTA: Buhari bai cire Buratai daga shugaban sojin kasa ba

6. Sojan ya na cikin wadanda su ka taimaka wajen nasarorin da a ka samu a yakin Boko Haram.

7. Adeosun ya shiga matsayi guda da babban Hafsun sojin kasar wanda ya ke Maigidansa a yanzu.

Kafin yanzu dai a na sa rai cewa Lamidi Adeosun zai yi ritaya kwanan nan. Sai dai wannan karin matsayi da a ka yi masa, ya fara nuna cewa akwai yiwuwar ya canji Janar Tukur Buratai a matsayin COAS.

Watakila sojan ya na kuma iya zama babban hafsun Sojin Najeriya gaba daya watau CDS, hakan zai faru ne idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami duka hafsun sojin a karshen sabon wa’adinsu.

A tarihi an taba samun Sojojin da su ka shiga mukami daya da hafsun sojojin lokacin su. Daga ciki akwai Janar Chika Obiakor, Joshua Dogonyaro, Aliyu Gusau, Garba Haladu, da kuma Garba Duba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng