Hukumar Soji ta sanar da bude kofar shiga makarantar sojoji NDA

Hukumar Soji ta sanar da bude kofar shiga makarantar sojoji NDA

- Makarantar tsaro ta sojoji ta sanar da cewa ta fara sayar da fom din shiga makarantar

- An bayyana cewa dukkan mai son shiga zai ziyarci wata kafar yanar gizo don cike bayanai

- Haka nan an bukaci masu son shiga da su tabbatar sun cika NDA a matsayin zabin farko na JAMB

Makarantar Tsaro ta Najeriya (NDA) ta ba da sanarwar buɗe kofarta don shiga cikin kwas na 73 na yau da kullum.

Masu sha'awar neman shiga makarantar na iya nema daga 23 ga Janairu zuwa 24 Afrilu, a cewar Magatakardar Makarantar, Brig.-Gen Ayoola Aboaba.

Aboaba, a cikin wata sanarwa a daren Lahadi, a Kaduna, ya ce an bude karbar shiga ne ga duk wadanda suka cancanta maza da mata ‘yan Najeriya.

KU KARANTA: 'Yan bautar kasa 13 sun kamu da COVID-19 a sansanin NYSC

NDA ta sanar da bude kofar shiga makarantar sojoji
NDA ta sanar da bude kofar shiga makarantar sojoji Hoto: The News Guru
Asali: UGC

Ya bayyana cewa masu sha'awar shiga zasu iya sayan form ta rcapplications.nda.edu.ng, kuma zasu biya kuɗi N3,500 ta REMITA.

Ya kuma shaidawa masu neman shiga NDA, dole ne su nuna shaidar rubuta jarabawar JAMB kuma dole ne su kasance sun zabi NDA a matsayin zabinsu na farko.

Ya ce an yi bayani dalla-dalla na abubuwan da ake buƙata na shiryawa don karatun digiri daban-daban.

KU KARANTA: Likitoci 3 sun mutu, 53 suna fama da Covid-19 a Kano

A wani labarin, Mohammed Adamu, Sufeto-janar na ‘yan sanda (IGP), ya ce an yaba wa jami’an 'yan sanda daga Najeriya da cewa su ne mafiya kwarewa a duniya saboda suna yin aiki fiye da takwarorinsu na kasashen waje idan aka ba su dama ta yadda za su gudanar da aikinsu.

Da yake magana a wani shirin Talabijin na Channels a ranar Litinin, Adamu ya ce ‘yan sanda a Najeriya suna yin abubuwa da yawa don wanzar da zaman lafiya, duk da rashin wadatattun kayan aiki da za su iya gudanar da aikin su, The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel