Fastocin kamfen din shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja

Fastocin kamfen din shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja

- Fastocin yakin neman zabe na gwamna Wike sun fara bayyana a babban birnin tarayya Abuja

- Shaidan gani da ido ya ga fastocin manne a jikin wasu gine-gine cikin babban birnin

- Rahoton ya bayyana shugaban kungiyar Rescue Nigeria Movement ne ya dauki nauyin watsa fastocin

Fastocin kamfen din shugaban kasa dauke da sunaye da hotunan gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, sun bayyana a babban birnin tarayya Abuja.

Wike, dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yana wa'adin sa na biyu kuma na karshe a matsayin gwamnan jihar Kudu maso Kudu.

Wakilin The Punch ya ga fastocin wadanda ke cikin nau'uka iri biyu a Abuja a safiyar ranar Litinin.

KU KARANTA: Ahmed Musa zai koma kungiyar kwallon kafa ta West Brom

Fastocin kamfen din shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja
Fastocin kamfen din shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja Hoto: The Punch
Asali: UGC

An sanya su a wurare masu mahimmanci akan shahararren titin Herbert Macaulay Way a cikin Babban Yankin Kasuwancin birnin.

Wasu an gansu an manna su a jikin katangar wani gini da ya kasance a matsayin Ofishin Kamfen din Shugaba Buhari da Osinbajo a 2015 da 2019.

An ga wasu a kusa da hedkwatar Kamfanin Man Fetur na Najeriya da kuma daura da Kwalejin Tsaron Najeriya da aka fi sani da War College.

Dangane da rubuce-rubuce a kan allunan mai taken "Kubutar da Najeriya 2023," Shugaban Rescue Nigeria Movement na kasa Jingiri Bala Mato ne ya samar da su.

Fastocin da ke dauke da tambarin PDP sun rubuta cewa, “Ka ceci Najeriya daga rashin tsaro, talauci, kashe-kashen 'yan fashi. Goyi bayan Cif Barr Nyesom Wike a matsayin Shugaban kasan Tarayyar Najeriya ta 2023. ”

Wakilinmu ya lura cewa an yi kuskuren rubuta sunan farko na gwamna, Nyesom, a matsayin "Nyemsom" a cikin fastocin biyu daban-daban.

Daya daga cikin fastocin yana ɗauke da hoton gwamnan sanye da kayan gargajiya na Kudu-Kudu tare da hular malafa don daidaitawa, yayin da yake sanye da kayan Arewa tare da hular da za ta yi daidai da hoton na biyu.

KU KARANTA: SERAP ta bukaci bayani kan N5,000 da za a bai wa 'yan Najeriya

A wani labarin, Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta yi zargin cewa rashin jajircewa daga bangaren Gwamnatin Tarayya ne ya haifar da karuwar tashin hankali a karo na biyu na annobar Covid-19 da ta addabi kasar, The Nation taruwaito.

Jam'iyyar ta zargi gwamnati da nuna halin ko in kula game da yaduwar annobar ta biyu, lamarin da ta ce, ya haifar da yaduwa da kuma karuwar mutuwa a kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel