Yanzu Yanzu: Buhari ya aika sunayen jakadu 42 majalisa domin tabbatar da su

Yanzu Yanzu: Buhari ya aika sunayen jakadu 42 majalisa domin tabbatar da su

- Shugaba Buhari ya aika jerin sunayen jakadu 42 zuwa majalisar dattawa

- Ana sanya ran majalisa za ta tantance sannan ta tabbatar da su

- Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa ne ya karanata wasikar Buhari a zauren majalisa a ranar Talata, 12 ga watan Mayu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sunayen jakadu guda 42 zuwa majalisar dattawa domin tantancewa da kuma tabbatar da su.

Legit.ng ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, wanda ya karanto jerin sunayen a ranar Talata, 12 ga watan Mayu, ya ce wadanda aka zaban sun kasance jami’ai a kasashen waje.

Yanzu Yanu: Buhari ya aika sunayen jakadu 42 majalisa domin tabbatar da su

Yanzu Yanu: Buhari ya aika sunayen jakadu 42 majalisa domin tabbatar da su Hoto: Vanguard
Source: UGC

Shugaban kasar ya ce za a tuwarwa majalisa takardun zababbun mutanen, inda ya kara da cewar wasu daga cikin sunayen sune Nwachukwu C. A.; A. Kefas; Y S. Suleiman; G.M. Okolo; G.E. Edopa, da sauransu.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanata wasikar Buhari a zauren majalisa a ranar Talata, 12 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Za mu bi diddigin yadda Buhari zai kashe bashin N1.3trn - Majalisa

A gefe guda kuma, mun samu labari cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta na kokarin dawo da ran babban kamfanin aikin karafunan nan watau Ajaokuta Steel Company Limited (ASCL) da ke jihar Kogi.

A ranar Litinin, 11 ga watan Mayu, 2020, aka nada wani kwamitin da zai dawo da kamfanin aiki.

Gwamnatin kasar ta na wannan yunkuri ne domin fadada tattalin arzikin Najeriya.

Wannan kwamiti da aka yi wa suna da Ajaokuta Presidential Project Implementation Team watau APPIT ya na kunshe da mutane 13 kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne shugaban wannan kwamiti. Mustapha ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta na da sha’awar farfado da wannan kamfani.

Ragowar ‘yan kwamitin su ne sakatarorin din-din-din na ma’aikatun ma’adanai da karafa, shari’a, da tattalin arziki.

Babban lauyan ma’aikatar shari’a ya na cikin wannan kwamitin. Ministan ma’adanai da karafa zai zama dayan shugaban kwamitin.

Saura su ne: Gabriel Aduda, Vincent Dogo, Farfesa Elegba S.B, Dr. Godwin Adeogba, da kuma shugaban MMSD.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel