Tinubu ya dawo Nigeria bayan batan dabon wata guda
- Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar APC, ya dawo gida Nigeria bayan shafe wata guda a waje
- Wasu rahotanni a farkon watan Janairu sun fara yada rahoton cewa an kwantar da Tinubu a wani asibitin kasar Faransa
- Daga baya, wata sanarwa daga Ofishin yada labaran Tinubu ta karyata rahotanni tare da bayyana cewa yana cikin koshin lafiya
Jagoran jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya dawo gida Nigeria bayan batan dabon wata guda.
An ga Tinubu a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas bayan saukarsa da yammacin ranar Lahadi, kamar yadda TheCable ta rawaito.
A farkon watan Janairu ne rahotanni suka fara cewa an kwantar da Tinubu a wani asibiti a kasar Faransa bayan ya kamu da rashin lafiya.
Wasu daga cikin rahotannin sun bayyana cewa Tinubu ya kamu da cutar korona, amma daga baya sanarwa daga ofishinsa ta karyata rahotannin.
KARANTA: Farfesa Jega ya amsa tambaya akan kokarin Buhari tun bayan hawa mulki
Sanarwar ta bayyana cewa Tinubu ya karbi sakamakonsa na gwaji tun a gida Nigeria kuma an sake gwada shi a waje amma duk ba'a same shi da kwayar cutar korona ba.
Sai dai, sanarwar ba ta yi wani karin haske dangane da dalilin fitar Tinubu waje ko takamaiman wuraren da ya ziyarta ba duk da hakan ba lallai bane a matsayinsa na dan kasa da yanzu babu wani mukamin gwamnati a hannunsa.
KARANTA: Hare-hare akan makiyaya: Miyetti Allah ta bawa gwamnatin tarayya wata shawara a fusace
Tuni wasu kungiyoyi suka fara bude ofisoshi tare da fara yakin nemawa Tinubu takarar kujerar shugaban kasa a 2023 a karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Duk da har yanzu Tinubu bai fito fili ya bayyana cewa zai yi takara ba, tuni makusanta da na hannun damarsa sun fara yi masa yakin neman zabe.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa Rochas Okorocha, tsohon gwanan jihar Imo, ya ce har yanzu yana nan daram a cikin APC tare da yin ikirarin cewa shugaba Buhari bashi da masaniyar wasu abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar.
A makon jiya ne toshon gwamnan wanda yanzu sanata ne a jam'iyyar APC ya sanar da cewa suna shirin kafa sabuwar jam'iyyar gabanin zaben 2023.
A cewar Rochas, wasu 'yan kanzagi sun shigo APc tare da kankane komai, kuma shugaba Buhari bai san wainar da ake toya ba a jam'iyyar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng