Ubale Yusufu ya na goyon bayan kujera ta koma yankin Kudu bayan mulkin Buhari
- Alhaji Hashim Ubale Yusufu ya na cikin manyan kusoshin APC a mataki na kasa
- Ubale Yusuf ya bayyana abin da ba a sani ba game da jam’iyyarsu dake kan mulki
- ‘Dan siyasar ya yarda mulki ya koma Kudu, ya ce an yi wannan yarjejeniya a baya
Hashim Ubale Yusufu ya yi wata hira da jaridar Daily Trust, ya tabbatar da cewa an yi yarjejeniya cewa mulki zai koma yankin kudu a shekarar 2023.
Mun tsakuro maku wasu daga cikin bayanan da aka samu a hirar da aka yi da ‘dan siyasar.
Da aka tambayi Ubale Yusufu a kan wanda za a mika wa mulki sai ya ce: “Ba alkawari aka yi a rubuce ba. Kusan wani abu ne mai kamar yarjejeniya.”
Ubale ya ce ya ji Bisi Akande ya na bayanin yadda su ka hadu da Muhammadu Buhari, su ka mara masa baya ya hau mulki, domin ya goyi bayansu nan gaba.
KU KARANTA: Samun mulkin Ibo zai sa a manta da Biyafara - Sam Ohuabunwa
“An yi yunkurin dunkule ACN da CPC a 2011, amma hakan bai yiwu ba. Daga baya a wani taro (a Jalingo), muka gane ana bukatar Buhari kafin a ci zabe.”
Mutumin jihar Jigawan yake cewa ya saurari jawabin Akande da kyau, daga nan fahimci cewa yarjejeniya aka yi (Buhari da Akande), za a goyi bayan juna.
A game da 2023, Ubale ya ce har yanzu APC ta na rike da Arewa, yayin da jam’iyyar ta fara samun magoya-baya a Kudu maso kudu da kuma Kudu maso gabas.
Jigon na jam’iyyar APC yake cewa matsalar ta na yankin Kudu maso yamma, domin maganar da ta ke nan ita ce za a mika masu mulki a zabe mai zuwa a 2023.
KU KARANTA: Buhari yace rashin kudi ya sa ya ke cin bashin
Alhaji Ubale ya ce ya na goyon bayan mulki ya koma Kudun, sai dai ya ce Muhammadu Buhari ba zai fito karara ya ce ga wanda zai gaje shi a jam’iyyar APC ba.
Ban da yarjejeniyar da aka yi, Ubale na ganin ya kamata ayi wa mutanen kudancin kasar sakayya.
Kwanakin baya mun kawo maku jerin manyan 'yan siyasan da ake ganin cewa zasu iya taimakon Bola Tinubu wajen samun kujerar shugaban Najeriya.
Daga cikin wadannan mutane akwai mai gima ataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.
Jigon APC a kasar Yarbawa, Bola Tinubu ya na cikin ‘yan siyasa da ake yi wa ganin suna hangen kujerar shugaban kasa a zaben 2023, amma babu tabbacin hakan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng