Ta’addanci: Wasu yan bindiga biyu sun shiga hannu a Zangon Kataf

Ta’addanci: Wasu yan bindiga biyu sun shiga hannu a Zangon Kataf

- Wasu mutane biyu da ake zaton yan fashi da makami ne sun shiga hannu a yankin Zangon Kataf da ke Kaduna

- Ana zargin Abdulhameed Abubakar Bala da Abubakar Abdulhameed Garba da hannu a wasu jerin hare-hare da aka kai al'umman Gora Gan, Damkasuwa, Zonzon da Kwaku

- A yanzu haka suna hannun sojoji yayinda ake gudanar da bincike

Dakarun Operation Save Haven sun kama wasu mutane biyu da ake zargin masu fashi da makami ne a kokarin kakkabe yan ta’addan da ke addaban mazauna Gora Gan, Damkasuwa, Zonzon da Kwaku a kananan hukumomin Zangon Kataf da Kauru da ke jihar Kaduna.

Wadanda ake zargin masu suna Abdulhameed Abubakar Bala da Abubakar Abdulhameed Garba, an kama su ne kan zargin kasancewa da hannu a wasu jerin hare-hare da aka kai kan garuruwan a watan Disambar shekarar da ta gabata.

KU KARANTA KUMA: Dakarun rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun kashe mutum 5

Ta’addanci: Wasu yan bindiga biyu sun shiga hannu a Zangon Kataf
Ta’addanci: Wasu yan bindiga biyu sun shiga hannu a Zangon Kataf Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

An kama su a tsakanin Ungwan Wakili da Zango Urban a karamar hukumar Zango Kataf a lokacin wani aikin hadin gwiwa tsakanin dakarun Operation Safe Haven da runduna ta musamman na hedkwatar tsaro.

A wani jawabi daga kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce wadanda ake zargin suna a hannun sojojin yayinda ake bincike, Daily Trust ta ruwaito.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya tuhumci wasu sarakunan gargajiya a jihar da yiwa gwamnatinsa zagon kasa wajen kokarin kawo karshen matsalar tsaron jihar.

Gwamnan, a wata ganawa da yayi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar ranar Alhamis, ya ce sarakunan gargajiya ba sa taka nasu rawan wajen yaki da yan bindiga.

KU KARANTA KUMA: Da’awar zaman lafiya: Malaman Kirista na arewa sun jinjinawa Sheikh Gumi

Ya ce hakan ya sa matsalar tsaro ta kara tsanani a jihar kwanakin nan, Premium Times ta ruwaito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel