Tsaro: Sarakunan gargajiya na yi min zagon kasa, Matawalle ya caccaki sarkin Anka

Tsaro: Sarakunan gargajiya na yi min zagon kasa, Matawalle ya caccaki sarkin Anka

- Gwamnan Matawalle ya mayar da martani ga sarkin Anka bisa jawabin da yayi

- Matawalle ya yi barazanar janye hannunsa daga sulhu da yan bindigan jihar

- Ya ce wasu sarakunan gargajiya na saba dokokin da yayi kan zama da yan bindiga

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya tuhumci wasu sarakunan gargajiya a jihar da yiwa gwamnatinsa zagon kasa wajen kokarin kawo karshen matsalar tsaron jihar.

Gwamnan, a wata ganawa da yayi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar ranar Alhamis, ya ce sarakunan gargajiya ba sa taka nasu rawan wajen yaki da yan bindiga.

Ya ce hakan ya sa matsalar tsaro ta kara tsanani a jihar kwanakin nan, Premium Times ta ruwaito.

Taron ya samu halartan Malaman addini, sarakunan gargajiya da yan jarida a gidan gwamnatin jihar dake Gusau.

Matawalle ya ce wasu sarakunan gargajiya na taimakawa kungiyoyin yan sakai a yankunansu duk da cewa gwamnati ta haramta, kuma hakan ya sa yan bindigan ke kai hari.

Bayan haka, gwamnan ya caccaki Mai marataba, Sarkin Anka, Attahiru Ahmad, kan jawabin da yayi cewa gwamnati ta amincewa mutane daukan makamai don kare kawunansu tun da gwamnati ta gaza waje kare al'umma.

KU KARANTA: Za mu fara yiwa duk mai son shiga Kano gwajin Korona, Ganduje

Tsaro: Sarakunan gargagiya na yi min zagon kasa, Matawalle ya caccaki sarkin Anka
Tsaro: Sarakunan gargagiya na yi min zagon kasa, Matawalle ya caccaki sarkin Anka Hoto: @presidency
Source: Twitter

KU KARANTA: Kotu ta jefa direba Kurkuku kan kashe N2m da aka tura masa cikin kuskure

Gwamnan yace "babu dadi a ce mutumin da ake ganin girmansa irin shugaban sarakunan gargajiyan jihar yayi hira da manema labarai yana kalubalantar kokarin da gwamnati da jami'an tsaro ke yi."

Matawalle ya ce hakkin tsaro na kowa ne ba na gwamnati kadai ba.

Ya ce idan mutan jihar da sarakuna basu son sulhun da gwamnatinsa da yan bindiga, sai janye hannunsa.

A bangare guda, wata kotu dake zaune a Ilori, birnin jihar Kwara, ya yankewa wani direba hukuncin shekaru biyu a gidan kaso kan amfani da kudin da ba nashi ba.

Direban, mai suna Adetunji Tunde Oluwasegun, ya yi amfani da kudi milyan biyu da wata mata Sherrifat Omolara Sanni ta tura asusun bakinsa na GTB cikin kuskure.

Ofishin hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da shi a kotun ranar Litinin, 18 ga Junairu, 2021.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel