Majalisar NEC ta yi zama, ta amince a shirya maganin COVID-19 a gida
- Majalisar NEC ta zauna a game da annobar Coronavirus a makon nan
- NEC ta bada dama masana su kirkiro maganin cutar a cikin Najeriya
- Gwamnati za ta hada kai da masanan ketare domin samun magunguna
Gwamatin tarayya ta hannun majalisar kolin tattalin arzikin Najeriya watau NEC, ta bada dama a kirkiro magungunan cutar COVID-19 a gida.
Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 21 ga watan Junairu, 2021, cewa an yi hurumi a fito da magungunan COVID-19 a Najeriya.
Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kuma bayyana cewa kofa a bude ta ke ga mutanen kasashen waje su shigo da maganin COVID-19 cikin kasar nan.
Fadar shugaban kasa ta ce majalisar NEC wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yake jagoranta tayi zama a jiya ta yanar gizo.
KU KARANTA: Za mu fara gwajin COVID-19 a kan iyakoki - Ganduje
Gwamnonin Najeriya wanda suna cikin wannan majalisa sun nesanta kansu daga Yahaya Bello, wanda ya fito ya na sukar magungunan COVID-19.
Kamfanin May & Baker da wani kwamitin gwamnati a karkashin Farfesa Oyewale Tomori ne suke kokarin fito da maganin wannan cuta a Najeriya.
Kwamitin Oyewale Tomori zai hada-kai da masanan cikin gida ko kuma na kasar waje domin ganin yadda al’umma za su samu maganin annobar.
Kawo yanzu annobar Coronavirus ta kashe mutane kusan 1, 500 a Najeriya. Wannan bai kai 1% na mutane miliyan biyu da cutar ta hallaka a Duniya ba.
KU KARANTA: Coronavirus ta na yi manai dauki dai-daya inji Gwamnan Imo
Gwamna Ifeanyi Okowa, ya yi wa ‘yan jarida magana bayan taron, ya ce ana kokarin ganin an fito da maganin, sannan ya ce NEC ba ta tunanin rufe gari.
Hukumar NPHCDA ta fito ta yi magana a makon nan, ta ce za a shigo da kwayoyi 100, 000 na maganin Coronavirus kafin a fara shirya su a cikin gida.
Shugaban NPHCDA, Faisal Shuaib ya bayyana haka yayin da 'yan jarida suka ziyarci wasu dakuna na musamman da aka yi tanadi domin ajiye magungunan.
Dr. Faisal Shuaib yace hukumar NAFDCA za ta duba nagartar maganin da za a kawo, kafin a raba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng