2023: Ba wata Biafra; Dattijo daga kabilar Igbo ya bayyana neman takarar shugaban kasa

2023: Ba wata Biafra; Dattijo daga kabilar Igbo ya bayyana neman takarar shugaban kasa

- Dattijo daga kabilar Igbo, Sam Ohuabunwa, ya bayyana aniyarsa ta neman takarar kujerar shugaban kasa a 2023

- A cewar Ohuabunwa, samun takarar dan kabilar Igbo zai kawo karshen hayaniyar Biafra da sauran hayaniya

- Ohuabunwa ya bayyana hakan ne ranar yayin taron rantsar da kungiyar 'sabuwar 'Nigeria' a Abuja

Sam Ohuabunwa, tsohon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin Nigeria (NESG) ya ce maganar Biafra zata kare a shekarar 2023 da zarar dan kabilar Igbo ya samu takarar kujerar shugaban kasa.

Da ya ke jawabi yayin rantsar da kungiyar 'sabuwar Nigeria (NNG)' ranar Laraba a Abuja, Ohuabunwa ya ce Allah ya saka masa niyya a cikin zuciyarsa ta bayyana aniyarsa ta yin takarar kujerar shugaban kasa.

An kafa kungiyar NNG a matsayin wata kafa ta tabbatar da hadin kai a kasa kuma ta kunshi mambobin jam'iyyu daban-daban, kamar yadda TheCable.

KARANTA: Katsina: An cafke mataimakin shugaban makarantar sakandire saboda yi wa daliba ciki

"Duk wani dan Nigeria mai kaunar hadin kai zai goyi bayan mulkin kasa yake kewayawa. Samun takarar dan kabilar Igbo zai kawo karshen hayaniyar neman kafa Biafra, duk wata hayaniya ma zata kare daga lokacin.

2023: Ba wata Biafra; Dattijo daga kabilar Igbo ya bayyana neman takarar shugaban kasa
2023: Ba wata Biafra; Dattijo daga kabilar Igbo ya bayyana neman takarar shugaban kasa @Thecableng
Asali: Twitter

"Ba zamu karbi mulki da niyyar daukan ramuwar gayya ko nuna banbanci ba, zamu zo da adalci. Zamu hada kai domin kawowa Nigeria cigaba.

KARANTA: Korona ta hallaka daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria, ya rasu ya bar Rolls Roys 10

"Allah ya dasa min a cikin zuciyata cewa na fito na yi takarar kujerar shugaban kasar Nigeria. Allah ya bani hikima da duk wata nagarta da ake bukata domin gyara Nigeria kowa ya ji dadi.

"Ba maganar Biafra ko yanki kudu maso gabas kawai ake yi ba; magana ce ta Nigeria," a cewarsa.

A cewar Ohuabunwa, Nigeria ta mallaki duk wani abu da kasa domin ta hada kafada da duk wasu manyan kasashe na duniya.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng