Buhari: Mu na karbo aron kudi ne saboda matsalar raguwar kudin shiga

Buhari: Mu na karbo aron kudi ne saboda matsalar raguwar kudin shiga

- Muhammadu Buhari ya kare gwamnatinsa a kan yawan karbo bashin kudi

- Shugaban kasar ya ce karancin kudin shiga ya sa gwamnati ta ke nemo aro

- A cewarsa, kudin shigan Najeriya ya ragu a cikin ‘yan shekarun bayan nan

A ranar Alhamis, 21 ga watan Junairu, 2021, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi magana game da bashin da gwamnatinsa ta ke yawan ci.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban kasar ya na cewa gwamnatin tarayya ta buge da neman bashi ne a sakamakon karancin kudi a halin yanzu.

A cewar shugaba Buhari, ana samun gibi a kasafin kudin Najeriya saboda yadda kudin shigar da gwamnatin tarayya ta ke samu ya sauka na wasu shekaru.

Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wannan bayani ne a wajen wani taro da aka shirya a fadar shugaban kasa domin tattauna maganar karbar haraji.

KU KARANTA: PDP ma ta karbo bashi - Minista ya kare Gwamnatin Buhari

Jaridar ta bayyana cewa an yi wannan taro ne ta kafar yanar gizo a Aso Villa a ranar Alhamis.

“Kamar yadda mu ke tsammani, wannan ya jawo bashin da ke kan Najeriya ya kai Naira tiriliyan 30, a watan Satumban shekarar 2020.” Inji shugaban kasar.

Buhari ya ce: “Wannan gibin da ake samu a sakamakon karyewar kudin shiga, ya sa mu ke yin wannan zama mai muhimmanci a kan maganar haraji.”

A wajen wannan taro, Buhari ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba ta da niyyar kara lafta haraji.

KU KARANTA: Za mu karbo bashin Tiriliyan 4.8 a shekarar 2021 - Buhari

Buhari: Mu na karbo aron kudi ne saboda matsalar raguwar kudin shiga
Buhari a taron FEC Hoto: Twitter Daga: @NGRPresident
Asali: Twitter

Sai dai shugaban Najeriyar ya yi kira ga al’umma su rika biyan haraji a matsayinsu na ‘yan kasa. Buhari ya bayyana irin kokarin da ya ke yi a wannan gabar.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta karbowa Najeriya aron kudi sama da Naira tiriliyan 18 daga 2015 zuwa shekarar 2020.

Alkaluma sun nuna cewa a shekaru biyar na mulkin APC, bashin kasar ya karu da fiye da 150%.

A karshen watan Yunin 2020 ne hukumar da ke kula da bashi na kasa watau DMO ta ce bashin da ke kan wuyan gwamnatin Najeriya ya haura Naira tiriliyan 30.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng